Gwamna Zulum ya kaddamar da wasu manyan ayyuka 23 a kudancin Borno

Gwamna Zulum ya kaddamar da wasu manyan ayyuka 23 a kudancin Borno

  • Gwamnan jihar Borno ya kaddamar da wasu sabbin ayyukan da gwamnatinsa tayi a yankin Borno ta kudu
  • A cewar majiyar Legit.ng Hausa, akalla ayyuka 23 ne gwamnan ya yi a wasu kauyukan dake yankunan
  • Daga cikin ayyukan da gwamnan ya kaddamar a ranar Laraba akwai na makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya

Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kaddamar da wasu ayyuka 23 a kudancin jihar Borno da suka hada da makarantu da asibitoci a wasu kauyuka da garuruwa.

Tun yammacin ranar Talata ne gwamna Zulum ya isa Biryel, hedkwatar karamar hukumar Bayo don fara aikin kaddamarwar, wanda tuni da safiyar yau Laraba ya fara a Bayo.

Gwamna Zulum wajen kaddamar da ayyuka
Gwamna Zulum zai kaddamar da wasu manyan ayyuka 23 a kudancin Borno | Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau, ya ce Zulum ya kaddamar da ayyuka 23 daga cikin sauran ayyuka da gwamnatin ta aiwatar a kudancin Borno.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi a jihar Nasarawa kan kisan wasu makiyaya

A sanarwar da gwamnatin jihar Borno ta fitar ta shafinta na Facebook, ayyukan sun hada da sabbin makarantun sakandire da firamare 13 da aka gina da kuma gyara su

Hakazalika da cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko guda shida da gine-ginen kananan hukumomi uku da suka hada da ofisoshin ‘yan sanda biyu da gidan gwamnati da kuma rukunin shaguna.

A cewar sanarwar:

"Ayyukan 23 sun kasance a kauyuka da garuruwan Hawul, Shani, Bayo da Kwaya Kusar a kudancin Borno."

Daga cikin makarantun da Zulum ya gina sun hada da:

"Sabuwar makarantar fasaha ta gwamnati mai girman ajujuwa 30, wata makarantar sakandare ta gwamnati mai ajujuwa 20, makarantar sakandaren al'umma mai ajujuwa 20, makarantar firamare mai ajujuwa 20 da dai sauransu."

Gwamna Zulum ya ba DSS umarnin kame malamai masu wa'azi ba tare da izinin gwamnati ba

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar kasar Amurka ta garkamawa Najeriya takunkumin sayen kayan yaki

A wani labarin, jaridar Punch ta rahoto cewa, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya umarci jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da su kamo duk wani malamin da ke wa’azi a fili tare da tunzura jama’a kan junan su.

Gwamnan, ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da masu ruwa da tsaki a taron tattaunawa kan yanayin tsaro na jihar wanda ya samo asali daga mika wuya na daruruwan mayakan Boko Haram a gidan gwamnati ranar Lahadi a Maiduguri.

A cewar gwamnan: “Wani muhimmin abu da nake son tattaunawa anan shine batun wa’azi a jihar. Idan ba a kula ba, wannan zai zama babban lamari saboda na ji masu wa'azi daban-daban sun fara cin zarafin juna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.