Majalisar dattawa ta gano N4.5bn na aikin barikin 'yan sanda a cikin kasafin NDLEA
- Majalisar dattawa ta bankado wasu makuden kudi har N4.5bn na aikin barikin 'yan sanda da aka cusa cikin kasafin NDLEA
- Shugaban kwamitin kula da miyagun kwayoyi, Sanata Hezekiah Dimka, ya ce sun gano hakan bayan duba takardun da ma'aikatar kudi suka kawo musu
- Ba wannan kadai ba, an gano wani bashi da ya dace gwamnatocin jihohi su biya na N16bn da aka lakabawa gwamnatin tarayya a cikin kasafin kudin shekarar nan
Majalisar dattawa a ranar Talata ta yi watsi da rahoton ta na kwamitin kula da miyagun kwayoyi kan cewa ta gano wasu kudi har N4.5bn da aka ware domin gina barikin 'yan sanda a kasafin shekarar 2022 a cikin kasafin NDLEA, Daily Trust ta ruwaito.
A yayin mika rahoton, shugaban kwamitin, Sanata Hezekiah Dimka, ya ce kwamitinsa ya gano wannan lamarin ne bayan duba takardun kasafin kudin da ma'aikatar kudi ta gabatar musu kuma suka gaggauta yin magana.
Kwamitin dubawa wanda ya samu shugabancin Sanata Barau Jibrin, ya yi watsi da rahoton kasafin NDLEA kuma ya bukaci kwamitin da ya koma tare da gyara matsalar.
Kwamitin majalisar dattawa kan muhalli wanda ke samun shugabancin Sanata Ike Ekweremadu, a ranar Litinin ya gano wasu kudi har N16bn da aka bukata a kasafin kudin 2022 domin biyan bashin da aka ciyo na aiwatar da aiki hukumar yaki da zaizayar kasa, NEWMAP.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daily Trust ta ruwaito cewa, Ekweremadu ya ce bashin an yi za a fara biyan shi ne bayan shekara goma wanda sai 2023 hakan zai cika.
Ya ce, bashin ya dace ne gwamnatocin jihohin da suka yi amfani da shi su biya ba wai gwamnatin tarayya ba.
NDLEA ta cika hannu da wani dillalin Miyagun Kwayoyi Da Hodar Iblis Na N2.3Bn a Abuja
A wani labari na daban, hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kama wani mai suna Okey Eze, kasurgumin dillalin miyagun kwayoyi a filin sauka da tashin jirage na Nnamdi Azikiwe, Abuja.
An damke Eze dauke da nadi 350 na hodar Iblis wanda kudin sa ya kai Naira biliyan biyu da digo uku (N2.3bn).
Hadimin shugaban hukumar, Mahmud Isa Yola, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Laraba, 22 ga Satumba, 2021.
Asali: Legit.ng