‘Yan bindiga sun sake kai hari Filato, sun kashe mutane biyu
- Wasu tsagerun 'yan bindiga da ake zaton makiyaya ne sun kai hari kauyen Ancha da ke yankin Miango a jihar Filato
- Maharan sun kai farmaki ne a ranar Talata, 23 ga watan Nuwamba, inda suka halaka wasu mazaje biyu a gonakinsu
- An tattaro cewa 'yan bindigar sun far ma mutanen da hari kafin suka raba su da ransu
Jihar Filato - Wasu 'yan bindiga da ake zaton makiyaya ne sun sake kai farmaki kauyen Ancha da ke yankin Miango a jihar Filato a ranar Talata, 23 ga watan Nuwamba, inda suka halaka mutane biyu.
SaharaReporters ta rahoto cewa mazajen biyu sun ci karo da makiyayan ne yayin da suke fitowa daga gonakinsu.
An kuma bayyana sunayen wadanda harin ya ritsa da su a matsayin Daniel James mai shekaru 32 da kuma Zakwe Deba mai shekaru 35.
A ruwayar Daily Trust, Davidson Malison, babban sakataren kungiyar ci gaban Irigwe na kasa (IDA), ya bayyana cewa an yi wa mamatan kautan bauna ne sannan aka kashe su a gonakinsu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wata majiya ta kuma bayyana cewa makiyayan sun farma mazajen biyu kafin suka kashe su. Ta kuma bayyana cewa an sanar da 'yan sanda jim kadan bayan afkuwar lamarin.
Karfin hali: Ƴan bindiga sun gargaɗi sojoji su fice daga wani gari a Filato domin za su kawo hari
A wani labarin, mun kawo a baya cewa Yan bindiga sun bukaci dakarun sojojin Nigeria su bar wuraren da suka kafa shinge a kusa da wani kauye a Miango, karamar hukumar Bassa a jihar Plateau.
A baya-bayan nan ne aka tura wasu sojoji zuwa yankin, bayan hare-haren da yan bindigan suke kai wa 'yan kauyen, The Cable ta ruwaito.
Sojojin da ke aiki karkashin Operation Safe Haven (OPSH), sun hana maharan kai wa yan kauyen hari.
Asali: Legit.ng