Da dumi-dumi: Gobara ta sake tashi a wata kasuwar Abuja
- An samu tashin gobara a kasuwar Nyanya da ke babbar birnin tarayya, Abuja, a daren ranar Talata, 23 ga watan Nuwamba
- Zuwa yanzu ba a san musababbin gobarar ba amma jami'an hukumar kashe gobara ta birnin tarayya na nan suna aikin saisaita annobar
- Hakazalika ba a rasa rai ba a gobarar wacce ta fara ci da karfe 8:00 na daren nan
Birnin tarayya, Abuja - Gobara ta tashi a kasuwar Nyanya da ke babbar birnin tarayya, Abuja, a daren ranar Talata, 23 ga watan Nuwamba, jaridar Vanguard ta rahoto.
Lamarin na zuwa ne kimanin makonni uku bayan gobara ta lakume akalla rayuka goma a shahararriyar kasuwar nan ta Kubwa.
An tattaro cewa ba a san abun da ya haddasa gobarar ba wacce ta fara da misalin karfe 8:00 na dare, kuma ba a rasa rai ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.
Tuni aka zuba jami’an hukumar kashe gobara ta birnin tarayya domin daidaita annobar.
A ruwayar gidan talbijin na AIT, an gano masu kashe gobara na zarya zuwa wajen afkuwar lamarin a babban titin Abuja-Keffi.
Kano: Gagarumar gobara ta kurmushe a kalla shaguna 41 a kasuwar Kurmi
A wani labari makamancin haka, mun kawo a baya cewa a kalla shaguna 41 ne suka kurmushe sakamakon gagarumar gobarar da ta tashi a fitacciyar kasuwar Kurmi ta jihar Knao a ranar Litinin, hukumar kashe gobara ta sanar.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Kurmi ta na daya daga cikin tsofaffin kasuwannin da ke garin Kano, cibiyar kasuwancin arewacin Najeriya.
Iblitala'in wanda ya fara wurin karfe 2 na dare, ya shafi shagunan masu siyar da litattafai a kasuwar.
Kamar yadda mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar, Alhaji Saminu Abdullahi yace:
"Mun samu kiran gaggawa daga wani Malam Baba Nasidi wurin karfe daya da minti hamsin da takwas na dare kan cewa gobara ta tashi a kasuwar litattafai.
"Bayan samun bayanin, mun gaggauta aika masu kashe gobara zuwa wurin inda suka isa karfe biyu da minti bakwai domin kashe gobarar."
Asali: Legit.ng