Dalla-dalla: Yadda zaku duba sakamakon jarrabawar WAEC na 2021 cikin sauki

Dalla-dalla: Yadda zaku duba sakamakon jarrabawar WAEC na 2021 cikin sauki

Bayan an samu jinkiri na yan makonni, hukumar shirya jarabawar kammala sakandare ta Afrika ta yamma (WAEC), ta saki sakamakon jarabawar da dalibai suka yi ta shekarar 2021, a ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamba.

Biyo bayan sakin sakamakon, hukumar shirya jarabawar ta saki jawabai kan yadda iyaye da dalibai za su iya duba sakamakon.

Daki-daki: Hanyoyi mafi sauki da mutum zai duba sakamakon jarabawar WAEC na 2021
Daki-daki: Hanyoyi mafi sauki da mutum zai duba sakamakon jarabawar WAEC na 2021 Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto
Asali: Getty Images

A wannan karon, daliban da suka rubuta jarabawar WASSCE ta 2021 basa bukatar siyar kati ko lambobi don duba sakamakon.

Yadda za a duba sakamakon jarabawar WASSCE na 2021/2022 a yanar gizo

Don duba sakamakon a yanar gizo, dalibai za su bukaci lambobin duba sakamako. Wadannan lambobi suna nan a jikin katin shaidar dalibai da suka yi amfani da shi wajen zana jarabawar, a cewar Patrick Areghan, shugaban WAEC na Najeriya.

Kara karanta wannan

Labari da Hotuna: DPO na yan sanda ya lashe gasar karatun Alkur'ani Izu 60 a jihar Kano

Da lambobin duba sakamakon, sai mutum ya shiga adireshin duba sakamakon WAEC sannan ya cike bayanan da aka lissafa a fam din.

Adireshin duba sakamakon shine: https://www.waecdirect.org/.

A takaice, don duba sakamakon WAEC a yanar gizo, kana bukatar wadannan abubuwan, a cewar shugaban harkokin jama’a na WAEC, Demianus Ojijeogu:

1. Lambar zana jarabawar WASSCE

2. Shekarar rubuta jarabawar

3. Lambar kati

4. Katin pin

Matakan duba sakamakon

1. Ka shigar da lambobi 10 na jarabawar WAEC dinka. (Wannan shine lambobin cibiyar jarabawarka 7 da kuma lambobinka na dalibi 3 misali. 4123456789)

2. Sai ka shigar da labobi 4 na shekarar da ka zana jarabawa misali. 2002

3. Ka zabi rukunin jarabawar

4. Ka shigar da lambobinka na e-PIN Voucher

5. Ka shigar da lambar shaidarka (PIN) a e-PIN

Kara karanta wannan

Hukumar NECO ta rike jarabawan dalibai sama da 80,000 a jihar Kano, Ta fadi dalili

6. Sai ka shigar da shi sannan ka jira shafin sakamakon ya fito

Yadda za ka duba sakamakon jarabawar WAEC ta sakon tes

A halin da ake ciki, hukumar shirya jarabawar ta ce dalibai na iya duba sakamakonsu ta sakon tes na waya, a cewar Channels TV.

Dalibai za su aika sako kamar haka:

  • WAEC*lambar jarabawa*PIN*shekarar jarabawa zuwa ga 32327(MTN, Airtel da Glo)
  • Misali: WAEC*4250101001*123456789012*2021
  • Ana shawartan dalibai da su bi tsarin da aka ambata a sama. Wannan na nufin ba sai sun bar tazara ba a sakon.
  • Bayan aika sakon, sakamakon zai iso gare ku ta lambar waya a kan N30.

Daga karshe: WAEC ta saki sakamakon jarabawar 2021 da aka yi

A baya mun kawo cewa hukumar shirya jarabawar kammala sakandare ta Afrika ta yamma, WAEC, ta saki sakamakon jarabawar da dalibai suka yi ta shekarar 2021.

TheCable ta ruwaito cewa, Patrick Areghan, shugaban hukumar jarabawar ta Najeriya, ya sanar da hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Ya ce jimillar dalibai 1,573,849 ne suka yi rijistar jarabawar a fadin Najeriya daga makarantu 19,425 da aka aminta da su. Yayin da dalibai 1,560,261 ne suka rubuta jarabawar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng