Dubun wani jagoran yan bindiga da wasu mutum uku ya cika a jihar Neja

Dubun wani jagoran yan bindiga da wasu mutum uku ya cika a jihar Neja

  • Gwarazan jami'an yan sanda sun samu nasarar damke wani kasurgumin limamin yan bindiga a Neja
  • Kakakin yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, yace mutumin ya amsa laifinsa tare da fallasa wasu sirrikan yan bindiga
  • Hakanan yace yan sanda sun samu nasarar kame wasu ɓarayin dabbobi, sun kwato wasu daga hannun su

Niger - Gwarazan yan sanda sun cafke wani ɗan shekara 50 a duniya, Umar Sama'ila, wanda ake zargin limamin duba na yan bindiga ne a wasu sassan Neja da Nasarawa.

Channels tv tace Kakakin rundunar yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, shine ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar a Minna, ranar Litinin.

Ya bayyana cewa an damke wanda ake zargin ne ranar Asabar bayan samun bayanan sirri cewa yan bindiga na shirin sace masu ibada a cocin Buku, yankin Abaji, Abuja.

Kara karanta wannan

Nasrun minallah: Jirgin yakin sojoji ya yi luguden wuta kan masu karban haraji na kungiyar ISWAP a Borno

Gwarazan yan sanda
Dubun wani jagoran yan bindiga da wasu mutum uku ya cika a jihar Neja Hoto: state.gov
Asali: UGC

Kakakin yan sandan yace:

"Yayin gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa ya kasance limamin duba na kasurguman yan bindiga da suka addabi Neja, Abuja da kuma Nasarawa."
"A tattaunawar da suka yi ta ƙarshe da tawagarsa a wannan ranar da aka cafke shi, ya umarce su, su kai hari cocin, kuma ya tabbatar musu zasu samu nasara."
"Ya kuma musu alƙawarin zai gudanar da addu'a domin a saki wani ɗan Bindiga 'Julli' dake tsare a hannun yan sandan Abuja."

Yan sanda sun cafke wasu 4

A cewar kakakin yan sandan, an damke Samaila ne kwana hudu kacal bayan jami'an yan sanda na caji ofis din Lapai sun samu nasarar kame wasu ɓarayin dabbobi.

Waɗan da jami'an suka kama sun haɗa da Abubakar Buba, Shehu Jare, Abubakar Garba, da kuma Abubakar Na'Allah, kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Nasarawa: 'Yan sanda sun bankado yunkurin sace jigon PDP

Kazalika Aboidun ya bayyana cewa jami'an yan sanda da taimakon yan bijilanti sun samu nasarar kwato shanu 40 da tumaki 15.

"Yayin bincike mutanen sun amsa cewa suna kiwon shanu ne a wannan dajin amma sun gaza bayyana yawan dabbobin da suka mallaka."

A wani labarin kuma Jirgin yakin sojoji ya yi luguden wuta kan masu karban haraji na kungiyar ISWAP a Borno

Jirgin yakin rundunar sojin sama NAF na Operation Haɗin Kai sun aika dandazon mayakan ISWAP Lahira a Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa sojin sun gano tawagar masu karban haraji hannun mutane, inda suka sakar musu ruwan bama-bamai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262