EFCC na neman wasu 'yan Nigeria 4 ruwa a jallo, ta saki hotunansu

EFCC na neman wasu 'yan Nigeria 4 ruwa a jallo, ta saki hotunansu

  • EFCC ta ayyan neman Akpodemaye Ikolo, Donald Olorunkoyede, Owootomo Tomilola Sunday, da Okuafiaka Bright Onyebuchi ruwa a jallo
  • Hukumar yaki da rashawar, a ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamban 2021 ta zargi mutanen da laifuka masu alaka da damfara
  • Hukumar, cikin sanarwar da ta fitar ta shawarci 'yan Nigeria su kai rahoto idan sun ci karo da wadanda ake neman ruwa a jallo

Hukumar yaki da rashawa da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta nemi taimakon 'yan Nigeria wurin neman wasu mutane hudu da ta ayyana nemansu ruwa a jallo kan damfara.

Hukumar a shafinta na Facebook, a ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamba ta ayyana neman Akpodemaye Ikolo, Donald Olorunkoyede, Owootomo Tomilola Sunday, da Okuafiaka Bright Onyebuchi ruwa a jallo.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: Jam’iyyar PDP ta sake rashi na wani babban jigonta

EFCC na neman wasu 'yan Nigeria 4 ruwa a jallo, ta saki hotunansu
EFCC na neman wasu 'yan Nigeria 4 ruwa a jallo, ta saki hotunansu. Hoto: EFCC
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

EFCC ta ce ana bincikar wadanda ake zargin ne kan laifuka masu alaka da damfara. Hukumar ta bukaci duk wani da ke da bayani mai amfani dangane da inda mutanen suke ya tuntubi ofisoshinta a kasar.

'Yan Nigeria sun yi martani

Wannan wallafar da hukumar ta EFCC ta yi ya dauki hankalin 'yan Nigeria inda suka bayyana mabanbantan ra'ayoyi.

Cardinal-Emmanuel Orji ya ce:

"Ku tura min katin waya da zan yi amfani da shi in kira ku idan na gan su."

Hassan Zakari:

"Da izinin Allah, nan bada dadewa ba za ku kama su."

Sadiq Aliyyu ya ce:

"Ko akwai wani tukwici da za a bayar bayan bada bayanai masu amfanin?"

Sadeeque Adam Sardauna ya ce:

"Ku saka tukwici da za ku bawa wanda ya gano su, za a gano su cikin gaggawa, mutane sun gaji da yin aiki a kyauta."

Kara karanta wannan

Bayan harin Lahadi, yan bindiga sun sake sace mutane ranar Litnin a titin Kaduna/Abuja

Abbas Musa ya ce:

"Ba abin da kuke tsinanawa, Yahoo boys sun cika gari amma ba ku daukan wani mataki a kai."

Motocci Fiye Da 50, Gidaje a Dubai Da Amurka: Jerin Kadarori Da Kuɗi Da Maina Ya Mallaka a Cewar EFCC

A baya kun ji cewa hukumar Yaki da Masu Yi wa tattalin arziki ta'annati, EFCC, ta yi nasara kan karar da ta shigar kan Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar yi wa tsarin fansho garambawul, PRTT, kan wawushe kudin fansho fiye da N2.1bn.

An samu Maina da laifuka kan zargi na 2, 3, 6, 7, 9 da 10 da EFCC suka tuhume shi da aikatawa, kana kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 8 a gidan gyaran hali.

Mai shari'a Okon Abang na Kotun Tarayya da ke Birnin Tarayya Abuja ya bada umurnin a kwace wasu kudade da kadarori mallakar Maina.

Kara karanta wannan

Yadda ‘yan mata 7 da ke dawowa daga Maulidi suka rasu a hatsarin jirgin ruwa a Jigawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164