Dalla-dalla: Adadin kudaden da jihohin Najeriya suka tara na harajin VAT a watanni 8 na 2021
- An tattara yawan harajin VAT da gwamnatin Najeriya ta tattaro daga jihohi 36 na kasar da babban birnin tarayya
- A rahoton da muka samo, an bayyana adadin kudin da kowace jiha ta tara a cikin watanni takwas na farkon 2021
- A baya dai an sha cece-kuce kan batutuwan da suka shafi kasafta harajin na VAT da jihohi ke tarawa da kansu
Najeriya - Daga watan Janairun bana zuwa Agusta, Najeriya ta tara harajin VAT da na biliyoyin Nairori daga dukkan jihohin kasar.
A rahoton da muka samo daga Daily Trust, an bayyana adadin kudaden da kowacce jiha ta kawo a cikin watannin takwas na farkon shearar 2021.
Duba da alkaluman tara harajin, jihar Legas da babban birnin tarayya Abuja ne suka fi kowacce jiha tara harajin na VAT a watannin.
A cikin wannan rahoton, Legit.ng Hausa ta tattaro daga The Cable yawan kudaden VAT da kowacce jiha ta tara kamar haka:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
- Abiya - N2.25bn
- Adamawa - N3.97bn
- Akwa Ibom - N9.31bn
- Anambra - N5.56bn
- Bauchi - N5.44bn
- Bayelsa - N13.22bn
- Benue - N1.42bn
- Borno - N3.08bn
- Kuros Riba- N1.90bn
- Delta - N13.48bn
- Ebonyi - N7.21bn
- Edo - N9.13bn
- Ekiti - N6.2bn
- Enugu - N5.19bn
- Gombe - N4.44bn
- Imo - N1.01bn
- Jigawa - N3.05bn
- Kaduna - N19.82bn
- Kano - N24.41bn
- Katsina - N4.64bn
- Kebbi - N1.22bn
- Kogi - N3.41bn
- Kwara - N3.48bn
- Legas - N421.20bn
- Nasarawa - N2.49bn
- Neja - N4.33bn
- Ogun - N11.60bn
- Ondo - N4.85bn
- Osun - N2.07bn
- Oyo - N61.05bn
- Filato - N5.43bn
- Ribas - N92.33bn
- Sakkwato - N4.59bn
- Taraba - N1.43bn
- Yobe - N9.34bn
- Zamfara - N762.55m
- Babban birnin tarayya - 241.10bn
Kano kadai ta tara harajin VAT da ya fi na yankin kudu maso gabas a 2021
A bangare guda, jihar Kano ta lallasa jihohin Kudu Maso Gabashin Najeriya guda biyar gaba dayansu wajen tara harajin VAT na watanni takwas na farkon shekarar nan ta 2021.
Wannan dai na zuwa ne biyo bayan cece-kucen da ake yi kan batun VAT, batutuwan da suka shafi shari'a da kuma tattaunawar siyasa tsakanin gwamnatin tarayya da wasu jihohi, musamman daga kudu.
Wani rahoto na musamman da Daily Trust ta samu ya nuna cewa, bayanan da aka samu na VAT daga Hukumar tara haraji ta FIRS, sun nuna cewa Kano ta tara N24.4b, fiye da kudaden da jihohi biyar suka tara na N20bn.
Asali: Legit.ng