Da duminsa: Mai kula da sarrafa jiragen sama ya yanke jiki ya fadi, ya mutu ya na tsaka da aiki

Da duminsa: Mai kula da sarrafa jiragen sama ya yanke jiki ya fadi, ya mutu ya na tsaka da aiki

  • Aniekan Inuk Effiong ma'aikaci ne da ke kula da sarrafa jiragen sama a filin sauka da tashin jirage da ke jihar Legas
  • Ma'aikacin ya yanke jiki ya fadi yayin da ya ke tsaka da aikinsa a sa'o'in farko na ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamba
  • Babu ko shurawa, Aniekan Inuk Effiong ya ce ga garinku inda ya rasu a take a yayin da ya ke bakin aikinsa

Legas - Aniekan Inuk Effiong mai kula da sarrafa jiragen sama ne da ke aiki da filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas.

Kamar yadda Daily Trust ta tattaro, Aniekan Inuk Effiong ya yanke jiki ya fadi kuma a take ya sheka lahira a sa'o'in farko na ranar Litinin yayin da ya ke tsaka da aiki.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun yi awon gaba da dimbin matafiya a hanyar Kaduna/Abuja

Da duminsa: Mai kula da sarrafa jiragen sama ya yanke jiki ya fadi, ya mutu ya na tsaka da aiki
Da duminsa: Mai kula da sarrafa jiragen sama ya yanke jiki ya fadi, ya mutu ya na tsaka da aiki
Asali: Original

An gano cewa ya na tsaka da aiki ya yanke jiki ya fadi kuma babu dadewa ya sheka barzahu.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel