Da Ɗumi-Ɗumi: An ritsa da uwa da matar kasurgumin dan bindiga, Bokkolo, yayin luguden wuta a Sokoto
- Mahaifiyar hatsabibin shugaban yan bindiga, Bokkolo, da matarsa suna cikin gida a yayin da jiragen yakin sojoji suka yi ruwan bama-bamai a gidan da ke Sokoto
- Ana fargabar akwai yiwuwar suna daga cikin wadanda suka mutu tare da wasu kwamandojinsa yayin harin da sojojin suka kai
- Majiyoyi da hukumar tsaro, mazauna gari da dan majalisa sun tabbatar da harin suna mai cewa jami'an tsaron sun samu gaggarumar nasara
Jihar Sokoto - Mata da mahaifiyar Bokkolo, hatsabibin dan bindiga suna cikin gidansa a yayin da jiragen yakin sojojin saman Nigeria suka yi luguden wuta a gidansa da ke Sokoto.
Daily Trust ta rahoto cewa jiragen yakin sun halaka yan bindiga da dama da 'yan uwansu.
Wani mazaunin unguwar wanda ya tabbatar da luguden wutan a gidan Bokkolo ya ce an kashe kwamandojinsa da dama a gidan.
Da Duminsa: Masu garkuwa sun kashe tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Majiyar ta ce:
"Amma ba mu tabbatar ko yana cikin wadanda suka mutu ba, amma matarsa da mahaifiyarsa suna gidan a lokacin da aka yi luguden wutan."
An far wa 'yan bindigan ne da ruwan wuta da aka fara musu tun ranar Juma'a.
An rahoto cewa wasu daga cikinsu sun tsere zuwa Tsabre, Sarkin Darai da Tidibale wadanda ke tsakanin Goronyo da Unguwan Lalle a Sokoto yayin samamen.
Harin na cikin wani atisaye hadin gwiwa ne da ya kunshi sojojin Nigeria, Sojojin Sama, Yan sanda, DSS da wasu jami'an tsaron.
A cewar wasu mazauna garin, sun gano wasu daga cikin 'yan bindigan da raunin bindiga a wasu kauyuka uku.
Majiya daga hukumar tsaro ta tabbatar da harin
Wani babban jami'in soja ya tabbatarwa Daily Trust cewa babban kwamandan 8 Division na rundunar sojojin Nigeria na Sokoto ne ke jagorantar samamen.
A cewarsa, an kashe daruruwar 'yan bindiga a kusa da unguwannin Isa da Sabon Birni kuma sojojin sun kai samamen har kusa da iyakar Nijar.
Ya kara da cewa an lalata dukkan maboyan 'yan bindigan.
Wata majiyar ta shaidawa Daily Trust cewa mafi yawancin wuraren da aka kai samamen na karkashin ikon hatsabibin dan bindiga Turji ne amma babu tabbas din cewa an kashe shi ko iyalansa a yanzu.
Yan sa kai guda hudu sun rasa rayyukansu yayin samamen kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.
Dan Majalisa Mai Wakiltar Sabon Birni ya magantu
Aminu Almustapha Gobir, dan majalisa mai wakiltar Sabon Birni ya tabbatar da labarin yana mai cewa wannan samamen na irinsa na farko a yankin.
Ya kara da cewa an samu nasarori sosai.
Ya ce:
"An kashe yan bindiga da dama kuma wasu daga cikinsu sun tsere da raunuka."
Wani mazaunin garin ya kara da cewa mazauna kauyukan suna taimakawa ta hanyar sanar da jami'an tsaro inda yan bindigan suke tserewa.
Asali: Legit.ng