Kano: ASUU ta yi barazanar maka Ganduje a kotu saboda 'sayar' da filayen Jami'a

Kano: ASUU ta yi barazanar maka Ganduje a kotu saboda 'sayar' da filayen Jami'a

  • Kungiyar malaman jami'o'i ASUU reshen Jami'ar Yusuf Maitama Suleiman ta koka kan kwace filaye da sayar da su da gwamnatin Kano ta yi
  • ASUU ta bakin shugabanta na jami'ar, Dr Abdulrazaq Ibrahim ta ce hakan ya sabawa wa yarjejeniyar FGN-ASUU da ta bawa jami'ar ikon cin gashin kanta
  • Kungiyar malaman ta ce abin da gwamnatin Kanon ta yi ya jefa dalibai da malamai cikin mawuyacin hali ta kuma shawarci a mayar da filayen ko ta tafi kotu

Kano - Kungiyar malaman jami'a a Nigeria, ASUU, reshen Jami'ar Yusuf Maitama Suleiman ta yi barazanar kai karar gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje kotu kan kwace wasu kayayyaki da filaye mallakar jami'ar.

Daily Nigerian ta rahoto cewa, shugaban ASUU na jami'ar, Dr Abdulrazaq Ibrahim, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar ya koka cewa gwamnan ya kwace wani gini da daliban koyon aikin likitanci ke zama a Kwanar Dawaki.

Kara karanta wannan

Budurwar da aka yiwa sharrin safarar kwayoyi a kasar Saudiyya ta zama jami’ar NDLEA

Ya ce hakan ya tilastawa malaman tsangayar neman matsuguni a wani karamin gini a main campus yayin da daliban kuma suke kai kawo tsakanin sabuwar ginin jami'ar da tsohuwar don karatu da zuwa dakin koyon aiki.

Kano: ASUU ta yi barazanar maka Ganduje a kotu saboda 'sayar' da filayen Jami'a
ASUU ta yi barazanar maka Ganduje a kotu saboda 'sayar' da filayen Jami'a. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar kungiyar, gwamnan ya kwace cibiyar koyar da ilimin sana'o'i da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a baya-bayan nan, tana mai cewa hakan ya kawo cikas ga koyar da dalibanta, rubuta JAMB da koyar da 'yan IJMB.

ASUU ta kuma ce Mr Ganduje ya mayar da wasu filayen jami'ar zuwa shaguna a wuraren da ba hakan aka tanada ba tana mai cewa hakan zai janyo matsaloli ga jami'ar a nan gaba, rahoton Daily Nigerian.

Har wa yau, kungiyar malaman ta ce gwamnan ya saba yarjejeniyar FGN-ASUU 2009 wacce ta tabbatarwa jami'ar cewa tana da ikon cin gashin kanta ba tare da katsalandan daga wasu ba.

Kara karanta wannan

Barazanar kora ta daga APC babban abun dariya ne, Sanata Marafa

Wani sashi na sanarwar ya ce:

"Gwamnatin jihar ta mayar da wasu filayen jami'ar da ke Main Campus zuwa shaguna kuma ba don haka aka tanade filin ba.
"Hakan zai lalata tsarin jami'ar na yanzu da nan gaba. Kuma saba yarjejeiyar FGN-ASUU 2009 ne wacce ta tabbatarwa jami'ar 'yancin kai."

Kungiyar ta ce za ta cigaba da bibiyar lamarin da nufin ganin ta ceci jami'ar daga rushewa ta kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki su kawo mata dauki.

"Sayar da filayen gwamnati da gwamnatin jihar Kano ke yi ba sabon labari bane. Abin da ya fi tada hankali shine kwacewa da sayar da filayen sabuwar jami'ar da ake fatan za ta girma," a cewar sanarwar.

Kungiyar ta bukaci a mayar da filayen da aka kwace tare da sayarwa a Jami'ar da ke kan titin Muhammadu Buhari Way da Kwanar Dawaki Campus da cibiyar koyar da ilimin sana'o'i da ke karamar hukumar Dawakin Tofa, idan ba haka ba za ta tafi kotu.

Kara karanta wannan

Ana zargin mai tsaron gidan yan kwallon matan Iran da namiji ce bayan buge fenariti biyu

‘Wanene Sarkin Cusa Kuɗi a Aljihu?’ Shekarau Ya Zolaye Ganduje Kan Bidiyon Daloli

A wani labarin, Sanata mai wakiltar Kano Central, Ibrahim Shekarau, ya caccaki gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, kan fitaccen bidiyon dalolli da ke nuna gwamnan yana soke dalolli a aljihunsa, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mr Ganduje ne ya fara sukar Shekarau a ranar 14 ga watan Oktoba yayin taron yan siyasa a Africa House, gidan gwamnati, a lokacin da ya zargi Shekarau da Sanata Barau Jibrin da 'karbar kudi a Abuja' ba tare da yi wa mutanensu komai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164