Dan Attahiru Bafarawa ya angwance da 'yar Janar Aliyu Mohammed Gusau

Dan Attahiru Bafarawa ya angwance da 'yar Janar Aliyu Mohammed Gusau

  • Dan Attahiru Bafarawa ya angwance da wata 'yar shahararre kuma jigo a gwamnati da tsaron kasar nan, Janar Aliyu Gusau
  • Abubakar Attahiru Bafarawa, ya auri 'yar tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a Najeriya
  • Abubakar Bukola Saraki ne ya bayyana halartar bikin da ya gudana a masallacin An-Nur da ke babban birnin tarayya Abuja

Abuja - Abubakar Attahiru Bafarawa, da ga shahararren dan siyasar Najeriya, Alhaji Attahiru Bafarawa ya angwance da amaryarsa Halima Aliyu Gusau.

Halima ta kasance diya ce ga tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Janar Aliyu Mohammed Gusau.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Abubakar Bukola Saraki ya bayyana halartar auren da kansa.

Dan Attahiru Bafarawa ya angwance da 'yar Janar Aliyu Mohammed Gusau
Bukola Saraki yayin bikin dan Bafarawa | Hoto: Abubakar Bukola Saraki
Asali: Facebook

Saraki ya halarci taron bikin, inda ya yada wasu hotuna da ke nuna wasu jiga-jigai a kasar su ma sun hallara.

Kara karanta wannan

2023: Na fasa tsayawa takarar shugaban kasa, Jigon PDP ya yi amai ya lashe bayan nema sau 3

Da yake bayyana halartar bikin a ranar Juma'a 19 ga watan Nuwamba, Saraki ya kuma yi wa ma'auratan addu'ar Allah ya dayyaba da kuma sanya albarka a auren.

A cewarsa:

"Da yammacin yau na hadu da iyalan tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Janar Aliyu Mohammed Gusau da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, a wajen daurin auren 'ya'yansu, Halimah Aliyu Gusau da Abubakar Attahiru Bafarawa, a masallacin An-Nur. , Wuse II, Abuja.
"Allah Ta'ala Ya albarkaci wannan gamayya ta gaske."

Kirkirar ajin WhatsApp na gyaran aure ya bar baya da kura

A wani labarin, wata malamar gyaran aure a Kano ta janyo cece-kuce kan karbar Naira 3,000 a matsayin kudin rajista ga mai son shiga ajinta na WhatsApp don koyar da zamantakewar aure.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Tinubu ya yi ganawar sirri da Orji Kalu a Abuja

Malamar, Fatima Fouad Hashim, wacce kuma ita ce ta kafa shafin Open Diaries ta ce ajin nata an kirkirareshi ne domin ‘yan aji su rika bayyana sirrinsu, su tattauna batun dangantaka da aure, inda ta bayyana cewa N3,000 ne a yanzu kudin zaman ajin na shekara daya.

Open Diaries sanannen dandalin sada zumunta ne a Facebook wanda galibi ’yan Arewa ke baje kolin sirrinsu, ba da labaran rayuwarsu, musamman kan batutuwan dangantaka da rikicin aure don sauran 'yan aji su tattauna akai da kuma bayar da shawarwari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.