Ndume ya yi bayanin dalilin da yasa sojoji suka ci galaba kan Boko Haram a Damboa

Ndume ya yi bayanin dalilin da yasa sojoji suka ci galaba kan Boko Haram a Damboa

  • Sanata Ali Ndume, shugaban kwamitin kula da rundunar soji ta majalisar dattawa, ya jinjinawa sojojin Birged ta 25 na rundunar Operation Hadin Kai
  • Kamar yadda yace, zakakuran sojojin sun samu nasarar cin galaba kan 'yan ta'addan Boko Haram ne saboda sabon tsari da hadin kan hukumomin tsaro
  • Ya ce jama'ar yankin sun matukar kara wa sojojin karfin guiwa ta yadda suka dinga musu wakokin yabo tare da murnar nasarar da suka samu
  • Ndume ya ce ya kira kwamandan rundunar yayin da ake kai harin, Birgediya Janar M. F. Babayo ya tabbatar masa da cewa sun shawo kan lamarin

FCT, Abuja - Shugaban kwamitin kula da rundunar sojin Najeriya a majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, ya jinjinawa runduna ta 25 ta Operation Hadin Kai kan yadda suka fatattaki 'yan ta'addan Boko Haram a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Mayaƙan Boko Haram sun sha mummunan kaye hannun sojoji, mutane na can suna murna a Damboa

Daily Trust ta ruwaito cewa, murna tare da shagali sun barke a Damboa bayan sojoji sun fatattaki 'yan ta'adda da suka kai farmaki garin wurin karfe 6:35 na safiyar Juma'a.

Ndume ya yi bayanin dalilin da yasa sojoji suka ci galaba kan Boko Haram a Damboa
Ndume ya yi bayanin dalilin da yasa sojoji suka ci galaba kan Boko Haram a Damboa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Tabbas wannan ya kawo tashin hankali ga mazauna yankin amma dakarun sojin sun yi musayar wuta da 'yan ta'addan, lamarin da yasa suka tsere tare da barin garin.

Ndume yayin jawabi ga manema labarai a ranar Juma'a a garin Abuja, ya ce nasarar an same ta ne saboda inganta hadin kai da tsari da aka yi tsakanin hukumomin tsaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya jinjinawa kwamandan rundunar, Birgediya janara M. F. Babayo da sauran sojojin da suka nuna zakakurancinsu wurin hana 'yan ta'addan kai wa Damboa farmaki.

"Na kira kwamandan rundunar a yayin da ake kai farmakin kuma cike na ji shi da kwarin guiwa. Ya sanar min da cewa ko a filin dagan, sun shawo kan al'amarin.

Kara karanta wannan

'Yan aware daga Kamaru sun shigo Najeriya, sun kashe mutane, sun kone gidaje

"Ba kamar a baya ba, yanzu sojojin a shirye suke kuma ba za su sassauta wa 'yan ta'adda ba za su dinga tunkararsu," yace.

Ya ce jama'a mazauna yankunan sun kara wa sojojin kwarin guiwa yayin da suke musu wakokin yabo da jinjina tare da murnar nasarar sojojin, Daily Trust ta ruwaito.

ISWAP sun tilasta wa manoman kauyukan Borno biyan haraji, sun ce zakkar gona ce

A wani labari na daban, jama'a masu zama wasu daga cikin kauyukan Borno sun koka da halin da suka samu kansu na tilascin biyan haraji da 'yan ta'adda suka saka musu a cikin zakkar amfanin gona.

Kamar yadda BBC ta wallafa, jama'a mazauna garin Damboa sun sanar da yadda 'yan ta'addan ke amfani da karfi wurin kwace amfanin gona da dabbobi, kuma biyayya a gare su ta zama dole domin tsira.

Wannan al'amarin ya kara fitowa ne a lokacin da ake cigaba da rade-radin cewa 'yan ta'addan ISWAP na amshe haraji daga wurin makiyaya da manoman jihar Borno.

Kara karanta wannan

Rundunar soji na bukatar sake dabarun yaki don yin nasara a kan yaki da ta’addanci - Dan majalisa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng