Ni da mahaifiyata muna kallo lokacin da aka zare ran kanina amma babu yadda muka iya - Dangote
- Mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya magantu a kan rasuwar dan uwansa, Sani
- Dangote ya bayyana cewa a kan idanunsa da na mahaifiyarsa aka zare ran kanin nasa suna ji suna gani amma babu yadda suka iya
- Ya ce abun da ya fi masu zafi shine lokacin da likitoci suka fada masu cewa saura masa awa daya ya bar duniya
Jihar Kano - Daga karshe mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya magantu a kan rasuwar kaninsa, Alhaji Sani Dangote.
Marigayin wanda ya kasance mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote, ya rasu a ranar Lahadi, 14 ga watan Nuwamba, a kasar Amurka bayan ya yi jinya.
Da ya tarbi jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a gidansa da ke Kano, a ranar Juma'a, 19 ga watan Nuwamba, Dangote ya ce mahaifiyarsu da yaran Sani na a wajen da aka dauki ran marigayin.
Ya ce ya fi masu radadi a lokacin da likitoci suka fada masu cewa dan uwansa na da kimanin awa daya da yayi masa saura kafin ya mutu, Daily Trust ta rahoto.
Dangote ya ce:
"Yana da radadi saboda ya mutu a gabana, a gaban mahaifiyarmu da kuma yara."
Ya ce shi da kansa saida zuciyarsa tayi rauni ganin ran dan uwansa yana fita daga jikinsa ta na'ura a asibitin.
Ya yi godiya ga Tinubu a kan ziyarar da ya kai masa, yana mai cewa ya ji dadin dangantakar yan uwantaka da ke tsakaninsa da ahlin Tinubu na tsawon lokaci.
Dangote ya ce rashin tabbas da ke tattare da mutuwa shi ne dalilin da ya sa ake so a kullum mutum ya dunga yin aikin alkhairi.
Ya kara da cewa:
"Yadda mutane ke ta zuwa abu ne mai matukar ban mamaki.
"Ziyarar zai taimaka mana wajen rage radadin musamman gareni saboda mun taso tare.
"Ya yi mana zafi sosai a lokacin da suka gaya mana cewa zai mutu nan da 'yan sa'o'i kuma dole ne mu kalli yadda numfashinsa na karshe ya fita."
A sakon ta'aziyyarsa, Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin dan Lagas kuma babban dan Najeriya.
Tinubu ya kuma bayyana cewa kudi baya siyan rai kuma babu abun da mutum zai iya yi idan lokaci yayi, rahoton Vanguard.
Ya yi kira ga iyalan marigayin da su dauki hakuri da ci gaba da yi masa addu'an samun dacewa.
An yi jana'izar Sani Dangote a Kano
A baya mun kawo cewa dubban musulmi sun hallarci jana'izar marigayi Sani Dangote, mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote, da aka yi a Kano a ranar Laraba.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa Imam Sani Muhammad na ya jagoranci sallar da aka yi wa marigayin a fadar sarkin Kano misalin karfe 11 na safe.
Imam Muhammad ya yi addu'ar Allah ya jikan marigayin ya kuma yafe masa kurakurensa ya kuma saka masa da gidan aljanna.
Asali: Legit.ng