Tubabbun yan Boko Haram sun yi zanga-zanga, sun gudu daga wuraren da aka ajiyesu
- Yan ta'addan Boko Haram da suka mika wuya sun ce gaskiya sun gaji da zama waje guda babu aiki
- Tubabbun sun gudanar da zanga-zanga inda suka lalata dukiyar gwamnati kuma har wasu suka gudu
- Har yanzu gwamnatin jihar Borno bata yi tsokaci kan wannan abu ba
Borno - Tubabbun yan Boko Haram da suka mika wuya ga Gwamnati sun yi zanga-zanga kan cigaba da ajiyesu waje guda a wasu sansani dake birnin Maiduguri, jihar Borno.
An tattaro cewa wasu daga cikinsu sun gudu daga wuraren da aka ajiyesu.
Majiyoyi sun bayyanawa AFP ranar Alhamis cewa wannan shine karo na hudu da tsaffin ta'addan suke zanga-zanga kan cigaba da tsaresu waje guda ba sa komai.
Daya daga cikin majiyoyin yace,
"Tsaffin yan Boko Haram din sun ce an ajiyesu waje guda tsawon watanni hudu ba su yin komai. Sun ce an raba su da matansu; wasu na da mata uku, wasu hudu."
"Sun lalata sansanin da aka ajiyesu lokacin zanga-zangan. Sunce Gwamnati ta sakesu idan ba tada wani shiri na musamman garesu."
Wata majiyar tace kimanin yan Boko Haram 250, mata da yara sun yi zanga-zanga a Gidan Taki inda suka fasa tagogin da kofofin sansanin.
Wani mai taimakawa Sojoji, Konto Garga, yace:
"Yan Boko Haram sun haukace mana da safen nan, sun fasa kofofi, tagogi kuma suna kokarin guduwa."
Wasu sun fara guduwa cikin gari
Jaridar Punch ta tattaro cewa tsaffin yan ta'addan sun gudu daga cikin sansanin.
Majiyar Punch tace:
"Wasu daga cikinsu na guduwa daga sansanin. Sun ce sun gaji da zama waje guda."
Amma kwamishanar harkokin mata, Hajiya Zuwaira Gambo, tace babu zanga-zangar da ta faru a sansanin.
Yan ta'addan Boko Haram 17,000 suka mika wuya kawo yanzu, Kwamdanda Operation Hadin Kai
Tiyata Kwamanda na rundunar “Operation Hadin Kai”, Christopher Musa, ya bayyana cewa adadin yan Boko Haram da suka mika wuya kawo yanzu ya kai 17,000.
Musa ya bayyana hakan ne ranar Juma'a lokacin da ya kai ziyara wajen shugabannin hukumar cigaban Arewa maso gabas, NEDC.
Ya bayyana cewa wannan adadi ya hada da mayaka, iyalansu da kuma wadanda aka tilasta shigar harkar Boko Haram.
Asali: Legit.ng