Miyagun ya bindiga sun hallaka mutun 213, sun yi garkuwa da wasu 676 a jihar Katsina

Miyagun ya bindiga sun hallaka mutun 213, sun yi garkuwa da wasu 676 a jihar Katsina

  • Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana alkaluman yadda hare-haren yan bindiga ya shafi mutane na tsawon wata huɗu
  • Sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa, yace an samu ragin kai hari tun bayan zartar da sabuwar doka kan tsaro
  • Inuwa yace gwamnati zata cigaba da ɗaukar matakai domin kawo karshen waɗan nan marasa son zaman lafiya a jihar

Katsina - Gwamnatin jihar Katsina, ranar Alhamis tace yan bindiga sun kashe mutum 213, sun sace 676 a faɗin kananan hukumomin da matsalar tsaro ta shafa, jihar Katsina.

This Day ta rahoto gwamnatin na cewa yan bindigan sun aikata wannan ta'adi ne tsakanin watan Yuli zuwa Octoba, 2021.

Gwamnatin ta kara da cewa a wannan tsawon lokacin jami'an tsaro sun samu nasarar damke mutum 724 da ake zargi da aikata ta'addanci kan mutane a jihar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga a Katsina sun koma sadarwa tsakaninsu da waya mai amfani da mitar rediyo ta Walkie Talkie

Jihar Katsina
Miyagun yan bindiga sun hallaka mutun 213, sun yi garkuwa da wasu 676 a jihar Katsina Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa, shine ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai game da cigaban da aka samu a dokar tsaro da gwamna ya sanya wa hannu.

Wane mataki gwamnati ta ɗauka kan waɗan da aka cafke?

Sakataren yace mutum 296 daga cikin waɗan da ake zargi suna gaban alkali, yayin da jami'an tsaro ke cigaba da binciken wasu 75.

Inuwa yace:

"A baki ɗaya alkaluman ayyukan yan bindiga, garkuwa da mutane da satar dabbobi daga farkon wannan doka zuwa yau, an samu raguwan kai hare-hare."
"Alal misali, a tsawon lokacin daga watan Yuli zuwa Agusta, mun samu rahoton sace mutane 173, wanda ya rutsa da mutum 475. Daga Satumba zuwa Oktoba an samu 61, ya rutsa da mutum 201."

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Tsagerun yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro sama da 100 a jihar Benuwai

"Yan bindiga sun kai hari sau 97 a watan Yuli zuwa Agusta, mutum 130 suka mutu wasu 56 suka jikkata, Haka kuma sun kai hari 56 daga Satumba zuwa Oktoba, 83 sun mutu wasu 58 sun jikkata."

Mutum nawa jami'an tsaro suka samu nasarar damke wa?

Sakataren ya cigaba da cewa:

"An cafke mutum 480 da ake zargi tsakanin watan Maris zuwa Satumba, 42 na karkashin bincike yayin da aka gurfanar da 216."
"Daga watan Satumba zuwa yanzun, jami'ai sun damke waɗan da ake zargi 244, 33 na karkashin bincike yayin da 80 ke gaban kotu."

A wani labarin kuma DPO na yan sanda ya lashe gasar karatun Alkur'ani Izu 60 a jihar Kano

A karon farko, kwamishinan yan sandan jihar Kano, Sama'ila Dikko, ya shirya musabakar Alkur'ani tsakanin dakarun yan sanda.

Mahaddatan jami'an yan sanda a mataki daban-daban sun fafata yayin musabakar, daga karshe aka bayyana waɗan da sukayi nasara.

Kara karanta wannan

Abun Mamaki: An kama mahaifi da abokinsa dumu-dumu suna lalata da 'yayansa mata biyu

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262