An tada hayaniya bayan wani farfesa a LAUTECH ya tuɓe wa wata ɗaliba hijabi a bainar jama'a

An tada hayaniya bayan wani farfesa a LAUTECH ya tuɓe wa wata ɗaliba hijabi a bainar jama'a

  • Akwai yiwuwar rikici zai barke a Jami'ar Fasaha ta Ladoke Akintola, Ogbomoso, a ranar Alhamis, 18 ga watan Nuwamba
  • Wasu al'ummar musulmi sun sha alwashin cewa ba za su lamunci cire hijabin da shugaban tsangayar koyar da aikin ma'aikatan jinya, Farfesa Ajibade Lawal ya yi wa wata daliba ba
  • An rahoto cewa Lawal ya zakulo wata daliba sanye da hijabi da Niqab yayin da ya ke bada misalin shiga wanda ba irin na ma'aikatan jinya ba

Ogbomoso, Jihar Oyo - Akwai yiwuwar rikici ya barke a Jami'ar Fasaha ta Ladoke Akintola, LAUTECH, da ke Ogbomoso, a ranar Alhamis 18 ga watan Nuwamba idan ba a dauki matakan dakile rikicin ba.

Wakilin Legit.ng da ke Ibadan, Ridwan Kolawole, ya bayyana cewa wasu kungiyoyin musulmi sun yi zanga-zanga kan abin da suka kira wuce gona da iri da Shugaban tsangayar Koyon Aikin Malaman Jinya, Farfesa Ajibade Lawal ya yi inda ya umurci wata daliba musulmi ta cire hijabi a bainar jama'a.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Shugaba Buhari Game da Barazanar ASUU

Ana tada hayaniya bayan wani farfesa a LAUTECH ya tuɓe wa wata ɗaliba hijabi a bainar jama'a
Ana tada hayaniya bayan farfesa a LAUTECH ya tuɓe wa wata ɗaliba hijabi a bainar jama'a. Hoto: LAUTECH
Asali: Facebook

Farfesa Lawal yana yi wa daliban tsangayarsa jawabi ne yayin wani taro na bude sashin koyarwa daga gida na LAUTECH tare da daliban tsangayar.

Yadda lamarin ya auku

A ranar Laraba, 17 ga watan Nuwamba yayin wani taro na daliban fannin jinya, Shugaban fannin jinya , Farfesa Lawal ya bayyana wa dalibai da kwararru a harkar jinyar irin shigar da za su dinga yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Farfesa Lawal ya ce hijabi ba ya cikin tsarin shigar da daliban jinya za su ci gaba da yi. An yi taron ne a wani dakin taro na LODLC da ke LAUTECH, don jami’ar ta samu damar tattaunawa da dalibai akan jarabawarsu da ke karatowa.

Yayin bayani akan shigar da dalibai mata za su dinga, ya kira wasu mata da ke sanye da hijabi sannan ya ce musu cewa shigarsu ba ta cikin tsari.

Kara karanta wannan

'Yan aware daga Kamaru sun shigo Najeriya, sun kashe mutane, sun kone gidaje

Wani ganau ya sanar da wakilin Legit.ng cewa shugaban makarantar ya kira wasu dalibai mata da ke sanye da hijabi, hakan bai gamsar da shi ba sai da ya kira wata da hijabinta ke da tsawo sannan ya yi sukar.

An bayyana yadda cikin takaici ya bayar da misali da dalibar inda ya ce tana ji yana neman wacce zai bayar da misali da ita ta makale gefe ta ki magana.

Majiyar wacce ta so a sakaya sunanta ta ce shugaban makarantar ya bukaci lambar rijistar dalibar sannan ya bata zabi 3.

Ya bukaci ko dai ta tafi kada ta sake dawowa sai wani zangon karatun, ko kuma ta dawo shekara mai zuwa ko kuma ta bar makarantar har abada.

Shugaban ya kara da cewa babu wanda ya isa ya dakatar da hukuncin da ya yanke. Majiyar ta kara da cewa dalibai da dama sun bi bayansa su na ba shi hakuri.

Kara karanta wannan

Muna ciyar da dalibai milyan 9 kulli yaumin a Najeriya, Minista Sadiya Farouq

A cikin wadanda su ka bi shi akwai manya daga cikin dalibai da kuma ita dalibar inda su ka duka guiwoyi kasa su na rokonsa, sannan dalibar ta mike daga durkusawar da ta yi ta kuma cire niqabin da ke fuskarta.

“Cike da alfahari mutumin ya ce babu wanda ya isa ya dakatar da hukuncin sa ko da kuwa gaba su ka kai shi,” a cewar majiyar.

Farfesa Lawal ya bayyana cewa shi musulmi ne kuma mai bin dokokin addinin.

Cece-kuce da barazana

Kungiyoyin musulmai ciki har da kungiyar musulman Najeriya sun lashi takobin kawo karshen karatun makarantar matsawar shugaban fannin jinya, Farfesa Ajibade Lawal bai bayar da hakuri ba.

Dalibai musulmai da ke zama cikin LAUTECH cikin takaici da alhinin abinda farfesan ya yi sun lashi takobin yin zanga-zanga in har ba a kawo gyara akan hukuncinsa ba.

Daya daga cikin wadanda ke shirin zanga-zangar ya yi tsokaci akan farfesan, inda ya ce:

Kara karanta wannan

Jami'ar Ilorin ta kori dalibin dan aji hudu da ya lakadawa lakcararsa dukan kawo wuka

“Haka halinsa ya ke, baku sani bane? Ko watan da ya gabata sai da ya mari wani dalibi.”

Hukumar jami’ar LAUTECH ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce ya faru ne a ranar Laraba, 17 ga watan Nuwamba kuma kwamitin bincike su na kokarinsu akai.

Kakakin jami’ar, Akin Fadeyi ya hori dalibai da su yi hakuri sannan su ci gaba da bin dokoki, su bai wa kwamitin bincike damar yin aikinta.

Fadeyi ya kara da cewa:

“Shugaban jami’ar na rikon kwarya, Farfesa Mojeed Olaide Liasu ya umarci shugaban kwalejin lafiya gabadaya, Farfesa Adeyemi da ya yi bincike mai zurfi dangane da al’amarin.”

Ya kara da cewa:

“Don haka hukumar makarantar ta ke horar da dalibai da su kasance cikin zaman lafiya yayin da su ke karatunsu sannan su bai wa masu bincike damar yin ayyukan su.
“Har ila yau, shugaban jami’ar ya tabbatar wa da kowa cewa babu wanda ya gagari hukunci.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: