'Yan kasuwa a Legas sun yi zanga-zangar nuna adawa da 'yar shugaban APC Tinubu

'Yan kasuwa a Legas sun yi zanga-zangar nuna adawa da 'yar shugaban APC Tinubu

  • Rahotanni daga jihar Legas sun bayyana cewa, wasu 'yan kasuwa sun fito zanga-zangar nuna adawa da 'yar Tinubu
  • An ruwaito cewa, 'yar Tinubu ta garkame wata kasuwa ne a jihar Legas bayan da aka gano gurbatar muhalli a cikinta
  • An ce ta sanya musu tarar Naira miliyan biyar tare da umartar 'yan kasuwar su gaggauta tsafta ce harabar kasuwar

Legas - Daruruwan ‘yan kasuwa ne a babbar kasuwar Oyingbo a ranar Laraba suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da Misis Folashade Tinubu-Ojo, diyar shugaban jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.

Tinubu-Ojo ita ce Iya Oloja Janar na Najeriya, PM News ta ruwaito.

An ce ta rufe kasuwar ne mako guda da ya gabata, saboda matsalar muhalli yayin da ta kulle dukkan harkokin kasuwanci.

Kara karanta wannan

'Yan aware daga Kamaru sun shigo Najeriya, sun kashe mutane, sun kone gidaje

'Yan kasuwa a Legas sun yi zanga-zangar nuna adawa da 'yar shugaban APC Tinubu
'Yan kasuwa yayin zanga-zanga | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

A cewar rahoton SaharaReporters, ta kuma ce 'yan kasuwar sai sun biya tarar N5m ga bayan da ta ba ‘yan kasuwar wa’adin kwanaki biyu su tsaftace harabar kasuwar.

Bayan an dade ana jiran bude kasuwar, ’yan kasuwar da yawansu sun fita kan titi a ranar Laraba, inda suka bukaci a sake bude ta.

‘Yan kasuwar a karkashin kungiyar ‘yan kasuwar Oyingbo, sun dauki kwalayen zanga-zanga a lokacin da suke ta rera wakar nuna adawa da Tinubu-Ojo da cewa "ba za mu lamunt ba, ba za mu lamunta ba."

Daya daga cikin kwalayen an rubuta:

“Folasade Tinubu-Ojo, diyar Tinubu, ki kyale Kasuwar Oyingbo, karamar hukumar Mainland, ku ji kukanmu, daukar nauyi, ‘yan kasuwar Oyingbo.”

Wani kuma yana cewa:

“Don Allah Folashade, ki sake mu daga bautar damu da ki ke.”

Kara karanta wannan

Dala tayi mummunan fadin da ta rasa N50 a ‘yan kwanaki, $1 ta koma N525 daga N575

Rikicin APC: 'Yan sanda sun mamaye sakateriyar jam'iyyar APC a Abuja

A wani labarin, adadi mai yawa na 'yan sanda cikin manyan motocin sintiri hudu ne suka mamaye hanyar shiga da fita a titin Blantyre da ke cikin sakatariyar jam’iyyar APC a Abuja.

An tattaro a ranar Laraba cewa ‘yan sandan da da jami'an tsaro na DSS suna wurin ne domin dakile yiwuwar tabarbarewar doka da oda.

Wakilin jaridar Punch ya samu labarin cewa jami’an tsaron sun taru ne bayan samun rahotannin tsaro game da shirin zanga-zangar da 'yan APC suka shirya yi na nuna adawa da yadda jam’iyyar ta gudanar da zabuka a taronta na gangami na jihohi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.