Labari Da Dumi-Dumi: An yi jana'izar Sani Dangote a Kano

Labari Da Dumi-Dumi: An yi jana'izar Sani Dangote a Kano

  • A yau Laraba 17 ga watan Nuwamba ne aka yi jana'izar marigayi Sani Dangote da Allah ya yi wa rasuwa a kasar Amurka
  • An yi wa marigayi Sani Dangote salla ne a fadar mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero misalin karfe 11 na safe
  • Manyan mutane daga gida da waje sun hallarci jana'izar cikinsu akwai Aliko Dangote, Abdussamad Isiyaka Rabiu, Bukola Saraki, Babagana Zulum ds

Jihar Kano - Dubban musulmi sun hallarci jana'izar marigayi Sani Dangote, mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote, da aka yi a Kano a ranar Laraba.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa Imam Sani Muhammad na ya jagoranci sallar da aka yi wa marigayin a fadar sarkin Kano misalin karfe 11 na safe.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar dattawa da manyan gwamnati sun isa jihar Kano domin jana’izar Sani Dangode

Labari Da Dumi-Dumi: An yi jana'izar Sani Dangote a Kano
An yi jana'izar Sani Dangote a Kano. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Imam Muhammad ya yi addu'ar Allah ya jikan marigayin ya kuma yafe masa kurakurensa ya kuma saka masa da gidan aljanna.

Manyan mutane daga gida da waje sun hallarci jana'izar

Wadanda suka hallarci jana'izar sun hada da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu, Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano da Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.

Saura sun hada da Gwamnan Borno, Babagana Zulum, Sanata Bukola Saraki, Shugaban SSS, Yusuf Magaji Bichi, Aliko Dangote, Abdussamad Isyaka Rabiu da manyan mutane daga gida da waje.

An birne marigayin ne a makabartar Sarari, inda ake birne iyalan gidan Dantata.

Sheikh Tijjani Bala Kalarawai, wanda ya jagoranci yin addu'a bayan birne marigayin ya bayyana shi a matsayin mutum mai saukin kai, da kyauta da karamci a yayin rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Allah ya yi wa mahaifin jarumi Umar Faruk Gombe rasuwa

Ya jadada bukatar da ke akwai na mutane su rika yi wa kansu hisabi a kowanne rana kafin su kwanta barci, don hakan zai taimaka musu su karu azama wurin aikin alheri tun suna raye.

An bayyana dalilin da yasa gawar Sani Dangote ba ta iso Najeriya daga Amurka ba

Tunda farko, kun ji cewa gawar marigayi Sani Dangote ba ta iso daga Amurka ba har a yammcin Talata sakamakon wasu cike-ciken takardu da ba a yi ba.

Wata majiya daga iyalan ta sanar da Daily Trust cewa ana tsammanin za a kawo gawar Kano a ranar Laraba.

An samu bayanai akan yadda lokaci ya tafi ba a taho da gawar Sani Dangote ba, kanin attajiri Aliko Dangote, sakamakon wasu takardu da ake ta cikewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164