Da Dumi-Dumi: Mutum 5 sun kone kurmus yayin da tanka makare da mai ta fashe a Ibadan-Legas
- Wani mummunan hatsari da ya yi sanadiyyar fashewar Tankar dakon mai ya lakume rayukan akalla mutun 5
- Rahoto ya bayyana cewa Tanka makare da man fetur ta yi taho mu gama da wata babbar mota a hanyar Ibadan-Legas
- Hukumar kiyaye haɗurra ta bayyana cewa tuni aka zuba jami'an kula da zirga-zirga domin magance faruwar wani hatsarin
Ogun - Jaridar Dailytrust ta rahoto cewa wata tankar dakon man fetur da ta fashe da safiyar Laraba ta lakume rayukan mutum 5 a kan hanyar Ibadan-Legas.
Rahoto ya nuna cewa waɗan da abun ya shafa, "Sun kone ta yadda ba za'a iya gane su ba," yayin da lamarin ya ritsa da su.
Lamarin fashewar tankar ya faru ne a kusa da gidan mai na Tunji Alegi, dake yankin Kwakyama, Ogere jihar Ogun.
Yadda hatsarin ya faru
Legit.ng Hausa ta gano cewa Tankar makare da man fetur ta yi taho mu gama da wata babbar mota, ta watse kuma ta fashe, inda ta cinye rayukan mutum 5.
Hakanan kuma an tabbatar da cewa aƙalla motoci biyar ne suka kone bayan fashewar Tankar a kan hanya, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
FRSC ta tabbatar da lamarin
Kakakin hukumar kare haɗurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Ogun, Florence Okpe, ta tabbatar da faruwar hatsarin ranar Laraba a Abeokuta.
Okpe ta bayyana cewa Tankar man ta yi taho mu gama da wata babbar mota, wanda ya jawo tashin wuta a wurin.
Ta yi zargin cewa lamarin ya faru ne daga, "Kokarin wuce mota ba bisa ƙa'ida ba da kuma tukin ganganci," ta bangare direban Tankar man.
Kakakin FRSC ta kara da cewa jami'ai sun tattara gawarwakin waɗan da suka mutu sun kai su ɗakin aje gawa a Ipara, karamar hukumar Remo.
Okpe tace:
"Mutum 5 sun kone kurmus ta yadda ba zaka iya gane su ba, mun gano gawarwakinsu kuma mun kai su Ipara zamu fitar da bayanai ba da jimawa ba."
Wane mataki aka ɗauka a kan hanyar?
Bugu da kari Okpe tace an zuba jami'an kula da zirga-zirga a kan hanyar domin guje wa faruwar wani hatsarin sanadiyyar na farko.
Ta kuma shawarci matafiya da direbobi su kwantar da hankulansu, kuma su baiwa jami'an da aka zuba haɗin kai.
A wani labarin kuma Basarake ya gwangwaje diyarsa da kyautar sabuwar mota bayan ta samu 'First Class,' Hotuna ya jawo cece kuce
Basaraken Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III, ya nuna farin cikinsa da ni'imar da Allah ya yi wa diyarsa a karatunta.
Diyar Sarkin, Gimbiya Zainab Adebunmi Adeyemi, ta kammala karatun digiri da sakamako mafi girma, ta samu kyautar mota. Hotunan motar da suka watsu a kafafen sada zumunta ya jawo cece-kuce daga bakin mutane.
Asali: Legit.ng