Shugaba Buhari ya dawo Najeriya bayan ziyarar aiki Birtaniya, Faransa da Afrika ta kudu
Shugaba Muhammadu Buhari ya dira babbar tashar jirgin saman Nnamdi Azikwe dake birnin tarayya Abuja da yammacin Talata, 16 ga watan Nuwamba, 2021.
Wannan ya biyo bayan ziyarar aikin da Shugaban kasan ya kai kasar Scotland, Faransa da Afrika ta kudu.
A kasar Scotland, Buhari ya halarci taron yaki da sauyin yanayi da Majalisar dinkin duniya ta shirya inda ya gana da Shugabannin kasashen duniya irinsu Emmanuel Macron na Faransa, Joe Biden na Amurka, da Yariman Birtaniya.
A faransa, Shugaban kasan ya halarci taron zaman lafiya da aka shirya kuma ya tallata Najeriya a idon yan kasuwa.
A taron ya gana da Shugabanni irinsu Muhammad Bazzoum na Nijar da Kamala Haris na Amurka.
A Afrika ta kudu kuwa, Shugaban kasan ya halarci taron bajakolin nahiyar Afrika inda ya sake tallata Najeriya ga masu zuba jari.
Asali: Legit.ng