Abubuwa 17 da ya kamata ku sani a rahoton da kwamitin Endsars ya gabatar
- Kwamitin bincike da gwamnatin jihar Lagas ta kafa domin tattauna lamarin wadanda jami'an SARS suka ci zarafi ya gabatar da rahotonsa
- Kwamitin ya gabatar da rahoton ne a ranar Litinin, 15 ga watan Nuwamba, inda ya bayar da shawarwari kan abubuwan da binciken nasa ya gano
- A bisa ga rahoton kwamitin, 'yan sanda da sojoji na da hannu dumu-dumu a harbin na Lekki Toll Gate a ranar 20 ga watan Oktoba, 2020
A shekarar da ta gabata, kwamitin bincike da gwamnatin jihar Lagas ta kafa domin tattauna lamarin wadanda jami'an SARS suka ci zarafinsu da sauransu ya saurari koke-koke kan zaluncin ‘yan sanda.
Hakazalika, kwamitin ya binciki lamarin Lekki tollgate da ake ta cece-kuce a kai.
A ranar Litinin, 15 ga watan Nuwamba, kwamitin karkashin jagorancin mai shari'a Doris Okuwobi mai ritaya, ya gabatar da rahotonsa mai shafi 309 a ofishin gwamna da ke Alausa, Ikeja.
EndSARS: Gwamnati ta yi karya, lallai an kashe dimbin matasa a Lekki Toll Gate, Kwamitin binciken jihar Legas
Sakamakon haka, kungiyar nan ta kare hakkin bil adama, Enough is Enough Nigeria, ta fitar da rahoton duk da cewar gwamnatin Legas ba ta yi hakan ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A wannan rahoton, Legit.ng ta kawo maku wasu muhimman abubuwa a cikin rahoton.
1. Harbin da aka yi wa masu zanga-zanga a Lekki Toll Gate a ranar 20 ga watan Oktoba, 2020 kisan gilla ne
2. 'Yan sanda da sojoji na da hannu a harbin
3. An tabbatar da mutuwar mutane tara
4. An yi zaton mutane hudu sun mutu
5. An gabatar da wasu gawarwakin mutane 96 ta hannun wani kwararren likita a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Legas, Farfesa John Obafunwa.
6. Mutane da dama sun ji munanan raunuka daban-daban
7. Gaba daya mutanen da abun ya ritsa da su sun kasance 48 amma suna iya fin haka
8. Jami'an 'yan sanda sun yi yunkurin yin rufa-rufa kan harbin masu zanga-zangar ta hanyar kwashe harsasai
9. Masu zanga-zangar sun gudanar da shi cikin lumana sannan suna ta rera taken kasa lokacin da aka far masu
10. Sojoji sun kwashe gawarwaki da dama na masu zanga-zangar da suka mutu, inda suka tafi da su a motocinsu
11. Harbin masu zanga-zangar da Sojojin Najeriya suka yi baya bisa ka'ida, ya wuce gona da iri, sannan ya kasance tsokana da rashin gaskiya
12. Kamfanin LCC ya ki samar da muhimman shaidu da za su taimaka wajen gudanar da bincike sannan ya yi kutse a bidiyon CCTV da bai cika ba.
13. Kwamitin ya bayar da shawarar hukunta jami'an sojoji da na 'yan sanda wadanda ke da hannu a harbi, jikkatawa da kuma kashe masu zanga-zangar lumana
14. Kwamitin ya kuma bayar da shawarar a bayar da hakuri ga masu zanga-zangar Endsars da aka kashe, wadanda aka jikkata, da kuma wadanda aka ci zarafi a yayin harin
15. Kwamitin ya ce ya kamata a hukunta shugaban ofishin 'yan sanda na Maroko da jami'an da aka tura kan laifin harbe-harbe da kashe masu zanga-zanga ba gaira ba dalili.
16. Kwamitin ya bayar da shawarar cewa a mayar da ginin Lekki Toll Plaza wurin tunawa da zanga-zangar ta hanyar canja masa suna zuwa #EndSARS Tollgate
17. Kwamitin ya bayar da shawarar cewa a mayar da ranar 20 ga watan Oktoban kowani shekara “toll-free day” idan har wajen zai ci gaba da kasancewa
Kwamitin da yake bincike a kan rikicin EndSARS yace dole a kawo Abba Kyari gabansa
A wani labarin, kwamitin da yake bincike na musamman a kan zargin cin zarafin mutane da ‘yan sanda suke yi, ya bukaci a kawo masa su Abba Kyari a gabansa.
Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto a ranar Talata, tace wannan kwamitin ya bada umarnin gurfanar da tsohon shugaban dakarun IRT, Abba Kyari. Kwamitin ya bukaci a kawo masa DCP Kyari a dalilin bacewar wani da ake zargi da laifi.
An kama wannan mutum ne a 2018, yanzu ba a san inda yake ba.
Asali: Legit.ng