Dalla-Dalla: Jerin matakan da zaka bi, ka mallaki gida a saukake a shirin cefanar da gidaje na FG

Dalla-Dalla: Jerin matakan da zaka bi, ka mallaki gida a saukake a shirin cefanar da gidaje na FG

  • A ranar Jumu'a 12 ga watan Nuwamba, Gwamnatin tarayya ta sanar da bude shafin intanet domin siyar da gidaje ga yan Najeriya
  • Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, yace jihohi 34 da babban birnin tarayya Abuja zasu samu damar shiga shafin
  • Mun tattara muku jerin hanyoyin da zaku bi, ku cike bayanan ku a wannan shafin domin amfana da shirin

Abuja - A ranar Jumu'a da ta gabata, 12 ga watan Nuwamba, gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin siyar da gidajen da ta gina ga yan Najeriya a farashi mai rahusa.

Gwamnatin ta bude sabon shafin yanar gizo domin mutane su nemi siyan ɗaya daga cikin gidajen kai tsaye daga inda suke.

A wurin kaddamar da shirin wanda a kaiwa lakabi da NHP, Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, yace mutane daga jihohi 34 da Abuja zasu samu damar shiga shafin yanar gizo.

Kara karanta wannan

Yadda aka yi ruwan sama a Masar, kunamai sun addabi mutane a cikin gidajensu

A cewar ministan, an kirkiri shafin ne domin tabbatar da yan Najeriya dake muradin mallakar gida, sun samu damar shiga tsarin.

Tsarin cefanar da gidaje
Dalla-Dalla: Yadda zaka cike fom ka mallaki gida a saukake sabon shirin samar da gidaje na Gwamnatin Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A halin yanzun, kimanin gidaje 5,000 aka kammala kuma za'a siyar da su a rukuni na 1 da na 2 a jihohi 34 da Abuja.

Rukuni na uku ba'a kammala shi ba, ana cigaba da aikin ginawa a jihohin Ribas da Legas. Daga cikin gidajen akwai masu ɗakin kwana ɗaya, biyu, wasu kuma na da uku.

Hakanan kuma farashin gidajen na tsakanin miliyan N9m zuwa miliyan N16m, ya danganta da wanda mutum ke so da kuma kuɗin da yake da su.

Legit.ng Hausa ta bi matakan da gwamnati ta saka a shafin, ta zo muku da bayani dalla-dalla kan yadda zaku cike.

Sharuddan da zaka cike kafin cike damar siyan gida

Kara karanta wannan

Yadda Buhari yake kashe makudan biliyoyi wajen sayen motoci, yana laftowa Najeriya bashi

A bayanan da muka samu a shafin NHP, wajibi ne ka cike waɗan nan sharudda dake tafe:

1. Babban mutum mai shekara sama da 18

2. Kana da cikakakken hanyar samun kudi ko ma'aikacin gwamnati

3. Ka kasance mai bada gudummawa a asusun samar da gidaje na ƙasa

4. Bin ka'idoji da dokokin mallakar gida wanda ya haɗa da cike fom a yanar gizo

Jerin abubuwan da ake bukata

1. Kananan hotuna: Karamin hotunanka wanda ka ɗauka kwanan nan masu girman JPEG, PNG.

2. Shaidar biyan haraji: Akwai bukatar ka gabatar da kwafin takardan shaidar biyan harajin na baya-bayan nan.

3. Katin bayanai (NIN, Lasisin tuki, fasfo): Ana bukatar kwafin katin bayanan ka mai girman JPEG ko PNG.

4. Takardar yabo daga bankin Mortgage ga masu amfani da bankin.

5. Takardan shaidar zuba kuɗi kashi 10% ga masu amfani da bankin Mortgage.

Jerin matakai 9 da zaka bi

Kara karanta wannan

Gumi ya caccaki 'yan aware: Igboho da Kanu ne suka kunna wutar rikicin Fulani a kudu

1. Bayan ka bude shafin, da farko zaka fara yin rijista daga nan zasu baka damar ganin gidajen dake akwai a sassa daban-daban na faɗin ƙasa.

2. Ka zabi jihar da kake so, sannan ka zabi gidan da ya kwanta maka a rai a jihar cikin waɗan da ke akwai. Bayan wannan ne zaka fara cike matakan neman mallaka.

3. Daga nan saika taɓa 'Apply,' hakan zai kai ka wani shafi da zaka cike sahihan bayanan ka da kuma na sana'arka ko aikinka.

4. Bayan haka, zaka dora abubuwan da muka zayyana maka a sama, sannan ka cike bayanan gidan da kuma shafin rantsuwa.

5. Mika takardan bukata: Daga nan sai ka danna 'Submit' domin tura fom ɗin da ka kammala cikewa.

6. Kudin fom: Bayan ka kammala tura duk bayanan daka cike a fom ɗin, da bayanan gidan da ka zaba, abu na gaba shine zaka biya dubu N10,000 kuɗin cike fom a yanar gizo.

Kara karanta wannan

El-Rufai na shan caccaka bayan da aka gano ya saba umarnin Buhari, ya yi amfani da Twitter

7. Matakan da zaka jira: Ma'aikatar ayyuka da gidaje ta ƙasa zata duba fom ɗin daka cike kuma ta tura takardar biyan kudi na gidan da suka zaɓa ga waɗan da suka samu nasara.

8. Biyan kuɗin gida: Da zaran ka samu sakon biyan kuɗi, ana tsammanin kodai ka biya kuɗin nan take ko ka haɗa kai da Mortgage Bank domin biyan kudin.

9. Abu na karshe, ma'ikata zata baiwa waɗan da suka samu nasarar bin dukkan matakan nan takardan mallakan gida.

Abin lura

1. Kudin da ka biya N10,000 wajen cike fom ba za'a dawo maka da su ba, ko da baka samu nasara ba.

2. Za'a yi watsi da fom ɗin ka matukar ka cike bayanan ƙarya.

A wani labarin kuma Batun Jaruma Rahama Sadau da wasu sabbin muhimman abubuwa 4 da suka faru a Kannywood

A wannan makon an samu wasu muhimman abubuwa guda 5 masu muhimmanci da suka faru a Kannywood.

Kara karanta wannan

Da dumi-daumi: 'Yan bindiga sun kai hari gefen FUT Minna, sun tafka mummunan barna

Daga cininsu shine batun raɗin sunan jaririyar da aka haifa wa Adam Zamgo, da kuma abinda ya shafi Rahama Sadau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262