Da Dumi-Dumi: Sojoji sun fatattaki 'yan bindiga daga wani gari a Kaduna
- Dakarun sojojin Nigeria sun kori wasu 'yan bindiga da suka shiga garin Zango da nufin kai wa mutane hari
- Lamarin ya faru ne a daren ranar Lahadi bayan sallar Isha'i misalin karfe 8 na dare inda 'yan bindigan suka yi wa garin zobe
- Miyagun sun fara harbe-harbe bayan zagaye garin kawai sai dakarun sojojin suka iso garin suka fattatake su har wajen gari
Jihar Kaduna - Sojoji sun yi galaba a kan wasu 'yan bindiga da suka yi niyyar kai hari a garin Zongo da ke karamar hukumar Zangon Kataf a daren ranar Litinin a Kaduna.
Malam Isa Tela, wani mazaunin garin Zango ya shaida wa Daily Trust cewa mutane suna harkokinsu bayan sallar Isha'i misalin karfe 8 na dare, kwatsam suka fara jin harbe-harben bindiga.
Ya ce hakan ya jefa mutane cikin fargaba a yayin da 'yan bindigan suka zagaye garin.
Ya ce:
"Mun fara jin harbe-harben bindigan ne misalin karfe 8 kusa da gidan mai na garin kafin suka zagaye garin daga kowanne bangare kafin sojojin suka iso suka tarwatsa su."
Ya ce babu wani labarin mutuwa ko rauni sakamakon harin a lokacin hada wannan rahoton.
Daily Trust ta ruwaito cewa an kashe mutane takwas a wasu hare-haren da aka kai a garuruwan Zangon Kataf a makon da ya gabata.
Rahoto: Masu ƙera wa Boko Haram bama-bamai sun koma dazukan Kudancin Kaduna
A baya, kun ji cewa shugabannin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga Bakoura Buduma sun mayar da masu hada musu bama-bamai dazukan yankin kudanci Kaduna, a cewar wani rahoton da PRNigeria ta fitar.
Karin Bayani: Bayan harin Islamiyya, Tsagerun yan bindiga sun sake mamaye Tegina, sun sace ma'aikata
A baya-bayan nan ne aka mayar da masu hada bama-baman da ake kira Amaliyyah a tsakin 'yan ta'addan, zuwa Rijana, Igabi da Chikun a yankin kudancin Kaduna.
Majiyoyi daga ciki sun ce kungiyoyin biyu na Boko Haram za su yi amfani da duwatsun da ke yankin a matsayin mabuya.
Asali: Legit.ng