Sheikh Gumi ya samo mafita ga lamarin 'yan bindiga, ya bude wa Fulani makaranta

Sheikh Gumi ya samo mafita ga lamarin 'yan bindiga, ya bude wa Fulani makaranta

  • Malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya bude wata sabuwar makaranta saboda karantar da makiyaya a dazuka
  • Ya bayyana cewa, ya kafa makarantar ne domin ya wanzar da zaman lafiya a yankunan Arewa maso yammacin Najeriya
  • Hakazalika, ya ya kira ga gwamnatin Buhari ta yi koyi dashi wajen ginawa makiyaya makarantar da za a wayar musu da kai

Kaduna - Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh (Dr.) Ahmad Gumi ya kafa makarantar makiyaya a cikin dajin Kaduna, inda ya dage cewa samar da ababen more rayuwa ga makiyaya a lungu da sakonsu zai taimaka wajen dakile munanan akidunsu.

Shehin malamin ya musanta batun cewarsa Najeriya ta zo karshe idan aka ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda, inda ya kara da cewa ana yi masa kuskuren fahimta.

Sheikh Gumi ya samo mafita ga lamarin 'yan bindiga, ya bude wa Fulani makaranta
Sheikh Ahmad Gumi | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Ya ce rashin tsaro a Najeriya, musamman lamarin ‘yan bindiga zai zama tarihi, domin ‘yan bindiga a shirye suke su yi watsi da makamansu idan aka samar musu da damammaki na ilimi da sauran ababen more rayuwa.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya har sun gaji da kuka, kashe-kashen rayuka ya zama ruwan dare: Yakubu Dogara

Ya sanya wa makarantar suna Sheikh Uthman Bin Fodio Centre, wacce ke dajin kiwo na Kagarko, kusa da Kauyen Kohoto a Jihar Kaduna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Vanguard ta ruwaito malamin na cewa:

"Idan cibiyar wacce aka tsara don ilimantar da makiyaya ta kasance kamar kowacce a cikin kasar, 'yan Najeriya za su zauna lafiya."

Makarantar Sheikh Gumi ne ya gina ta a karkashin gidauniyar Mosque Foundation Limited, Kaduna.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin Buhari da ta yi koyi da wannan aikin, inda yace, zuba kudade wajen ilmantar da makiyaya ya fi sayen makamai don yakar 'yan bindiga.

Jaridar Today ta ruwaito malamin na bayyana cewa, ya gina makarantar ne domin wanzar da zaman lafiya a yankunan da rikicin bindiganci ya lalata a Arewacin Najeriya.

Ya kara da cewa:

“Idan sun yi ilimi, ba za su yi abin da suke yi ba.

Kara karanta wannan

Gumi ya caccaki 'yan aware: Igboho da Kanu ne suka kunna wutar rikicin Fulani a kudu

Legit.ng Hausa ta sha ruwaito muku yadda ake artabu da Sheikh Gumi kan batutuwan da suka shafi 'yan bindiga, inda malamin ke nuna goyon baya da tausaya musu.

Sabon hari: 'Yan bindiga sun farmaki mazauna a Sokoto, sun hallaka mutane da yawa

A wani labarin, akalla mutane 15 ne ‘yan bindiga suka kashe yayin wasu sabbin hare-haren da suka kai wasu kananan hukumomi biyu a jihar Sokoto, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Gwamnan jihar, Aminu Tambuwal, wanda ya tabbatar da harin a ranar Litinin, ya bayyana cewa kananan hukumomin da abin ya shafa sune Goronyo da Illela.

Ya bayyana cewa an kashe mutanen yankin ne a lokacin hare-haren da suka auku tsakanin daren Lahadi zuwa safiyar Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.