Borno: Arangama ta da 'yan ta'addan ISWAP a kan titi, Malamin makaranta
- Wani malamin makaranta a Damboa da ke Borno ya sanar da arangamarsa da miyagun 'yan ta'addan ISWAP
- Ya ce suna harkarsu a kan titi kamar yadda sojoji ke yi, kuma da suka tambaye shi waye shi, yace shi dan kasuwa ne
- Sun bashi kudi inda suka umarce shi da ya siyo musu omo, biredi da takalmi, sun kuma ba direba kyautar kudi har N7,200
Damboa, Borno - Wani malamin makaranta da ke zama a karamar hukumar Damboa a jihar Borno ya bayyana yadda suka yi arangama da mayakan Islamic State in West Africa Province (ISWAP).
Malamin wanda ya bukaci a boye sunan sa, ya ce sun yi gaba da gaba da 'yan kungiyar yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa karamar hukumar Biu ta jihar a cikin kwanakin nan.
"Hankalinsu kwance suke yin komai kamar babu komai," yace.
"Direbanmu ya sanar da mu cewa kada mu tsorata lokacin da ya ga sun tunkaro mu. Suman zaune na yi amma a haka na samu kwarin guiwa. Sai na ji suna tambayata waye ni? Na sanar da su cewa ni dan kasuwa ne.
"A take suka bani kudi in siyo musu omon wanki, biredi da kuma takalmi. Ya bai wa direbanmu kyautar dubu bakwai da dari biyu kuma yace ya bashi kyauta ne," yace.
Wani mutum mai tafiya a titin ya tabbatar da cewa akwai mayakan ta'addancin ISWAP a titunan yankin, Daily Trust ta wallafa.
"Suna da wurin duba motoci har uku a kan hanyar Damboa zuwa Biu na tsawon lokaci.
“Su kan tsare masu kaiwa da kawowa kuma su duba motocinsu idan akwai wani jami'in tsaro ko masu tallafi a ciki. Ba su sassauta musu," yace.
Daily Trust ta ruwaito cewa, muguwar kungiyar 'yan ta'addan a ranar Asabar wurin karfe 9 na safe sun kai harin kwanton bauna ga dakarun soji a garin Askira da ke karamar hukumar Askira Uba ta jihar Borno.
Sun halaka birgediya janar 1 da wasu sojoji hudu a mummunan farmakin. Har ila yau, sun saka shinge a kan babban titin Damboa zuwa Biu.
Mayakan ISWAP na sake hada kansu a wurin tafkin Chadi, Ndume ya koka
A wani labari na daban, shugaban kwamitin kula da sojoji na majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, ya koka kan yadda miyagun 'yan ta'addan Islamic State West Africa Province (ISWAP) ke sake shirya kansu a yankin tafkin Chadi.
Ndume, wanda ke wakiltar mazabar Borno ta tsakiya a majalisar dattawa, ya yi wannan koken yayin da ya ke tattaunawa da manema labarai a ranar Lahadi yayin martani ga harin da 'yan ta'addan suka kai Askira Uba a jihar Borno a ranar Asabar.
Daily Trust ta ruwaito cewa, soja mai mukamin birgediya janar da wasu sojoji uku ne suka sheka lahira a yayin da aka kashe 'yan ta'adda masu yawa a kan hanyar.
Asali: Legit.ng