Da Duminsa: ISWAP ta karyata Rundunar Sojojin Nigeria, ta bayyana adadin sojojin da ta kashe a harin Askira
- Kungiyar 'yan ta'addan ISWAP ta karyata Rundunar Sojojin Nigeria game da adadin mutanen da suka mutu a harin Askira
- A yayin da Rundunar Sojojin ta ce dakarunta uku kacal aka kashe, ISWAP ta yi ikirarin cewa sojoji 17 ta kashe yayin harin
- Rundunar sojojin ta Nigeria ta dade tana cewa ta yi galaba a kan 'yan ta'addan amma a baya-bayan nan suna ta kai hare-hare
Borno - Mayakan kungiyar ta'addanci na ISWAP da suka balle daga Boko Haram sun ce sojoji 17 suka kashe yayin harin da suka kai a Askira, karamar hukumar Askira ta jihar Borno, SaharaReporters ta ruwaito.
Legit.ng ta ruwaito yadda mayakan ISWAP suka yi artabu da dakarun sojojin Nigeria a sansaninsu.
Wasu fararen hula sun ce sun hango mayakan ISWAP sunyi jerin gwano a hanyar zuwa Ngude a hanyar Askira.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Fararen hulan sun kara da cewa sun hangi yan ta'addan sun nufi inda sojojin suke amma ba a dauki mataki ba har sai da kungiyar ta isa garin Askira.
Bayan awanni ana fafatawa, mai magana da yawun rundunar sojoji, Onyema Nwachukw ya ce an kashe Birgediya Janar da wasu sojoji guda uku.
Ya bayyana sunan Birgediya Janar Dzarma Zirkusu, amma bai ambaci sunan sauran kananan sojojin ba.
ISWAP ta karyata rundunar sojojin
Amma, ISWAP cikin sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi da dare ta yi ikirarin cewa sojoji 17 aka kashe.
A cewar kungiyar, an kashe sojoji 13 a lokacin da mayakan ta suka kai hari sansanin sojoji a Askira yayin da an kashe wasu hudu ciki har da Birgegiya Janr Zirkus yayin harin kwanton bauna a Balguma, kusa da Askira.
ISWAP ta kara da cewa ta kona sansanin sojoji da ke garin Askira, da motar sojoji da tankin yaki da ke ajiye cikin sansanin.
Yan ta'addan sun kuma sace wani motar sojojin, tankin yaki, makamai daban-daban da bindigu yayin harin.
Tun bayan mutuwar shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, ISWAP tana ta mamaye wurare a Tafkin Chadi.
A baya-bayan nan, kungiyar ta nada Wali Sani Shuwaram, mai shekaru 45 a matsayin sabon shugabanta a Tafkin Chadi.
ISWAP ta kara karfi bayan daruruwan yan Boko Haram karkashin Shekau sun koma gefen ISWAP.
Rundunar sojojin na Nigeria ta sha nanata cewa ta ci galaba a kan 'yan ta'addan amma a baya-bayan nan, 'yan ta'addan na yawan kai hare-hare.
Kungiyar ta yi sanadin rasuwar fiye da mutum 50,000 ta kuma raba miliyoyin mutane da gidajensu a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.
Rahoto: Masu ƙera wa Boko Haram bama-bamai sun koma dazukan Kudancin Kaduna
A baya, kun ji cewa shugabannin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga Bakoura Buduma sun mayar da masu hada musu bama-bamai dazukan yankin kudanci Kaduna, a cewar wani rahoton da PRNigeria ta fitar.
A baya-bayan nan ne aka mayar da masu hada bama-baman da ake kira Amaliyyah a tsakin 'yan ta'addan, zuwa Rijana, Igabi da Chikun a yankin kudancin Kaduna.
Majiyoyi daga ciki sun ce kungiyoyin biyu na Boko Haram za su yi amfani da duwatsun da ke yankin a matsayin mabuya.
Asali: Legit.ng