Yadda aka yi ruwan sama a Masar, kunamai sun addabi mutane a cikin gidajensu
- An yi ruwan sama a kasar Masar, alamarin da ya tono kunamai masu dafi da suka addabi yankin Aswan
- A halin da ake ciki, rahotanni sun bayyana cewa, mutane uku ne suka mutu yayin da da yawa suke kwance a asibiti
- Ruwan saman ya kai lalacewar wutar lantarki a yankin, tare da lalata gidaje da gonaki da yawa a Aswan
Aswan, Masar - Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ambaliya a Aswan na kasar Masar, sun koro kunamai zuwa neman mafaka a gidajen mutane.
Mutane 3 ne AlJazeera ta ruwaito suka mutu inda sama da 400 ke kwance a asibiti a fadin jihar domin karbar maganin dafin kunama, a cewar kafafen yada labarai na gwamnati.
Sai dai kuma mukaddashin ministan lafiyan kasar, Khalid Abdel-Ghafar ya ce a cikin wata sanarwa da ya fitar, ba a samu rahoton mace-mace ko daya ba.
Ma’aikatar lafiya ta kasar ta tabbatar wa da jama’a cewa tana da isassun adadin maganin dafin, inda ta ce an samu allurai 3,350 a Aswan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mamakon da ambaliyar ruwa ya kuma tilastawa hukumomin yankin dakatar da makarantu a ranar Lahadin da ta gabata, in ji gwamna Ashraf Atia.
Mutanen da kunamai suka harba sun ce alamomin da suke ji sun hada da zafi mai tsanani, zazzabi, gumi, amai, gudawa, ciwon jiki, da juyawar kai.
Tsaunukan Aswan yanki ne mai yawan kunaman Larabawa masu fadin wutsiya wadanda aka fi sani da Androctonus crassicauda, wanda ke nufin "mai kisan mutum" a yaren Girkanci.
Ana la'akari da su a cikin kunamai mafi hadari a duniya, tare da dafin da zai iya kashe mutum a cikin sa'a guda bayan harbi. Abu ne sananne cewa, harbinsu yana haddasa mutuwar mutane da dama a shekara.
Nau'in kunaman na da tsayin inci 3-4 kuma suna dogara ne da jijjiga da sauti don gano abin da suke hari kasancewar ba sa gani, ji ko jin kamshi.
Hotuna da faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna cunkoson tituna da lalatattun gidaje da ababen hawa da gonaki.
Ruwan sama ya kuma haifar da daukewar wutar lantarki.
Kalli hotuna da bidiyo:
Yadda Tarayyar Turai ta kashe £130m wajen tallafawa 'yan gudun hijira a Borno
A wani labarin, Kungiyar Tarayyar Turai ta hanyar shirye-shiryenta na tallafi ta farfado da rayuwar miliyoyin mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a jihohin Borno da Arewa maso Gabas, in ji shugabar tawagarta a Najeriya da ECOWAS, Ambasada Samuela Isopi.
Ta ce kungiyar ta EU ta bada kudi kusan Yuro miliyan 130 a cikin shekaru hudu da suka gabata don tallafawa kokarin gwamnatin jihar Borno na sake ginawa da kuma gyara al’ummomin da abin ya shafa, Leadership ta ruwaito.
Wannan tallafin kudade kadai, a cewarta, ya taimaka wajen maido da ababen more rayuwa a fannoni da yawa.
Asali: Legit.ng