Yadda Najeriya ta shigo da kifin sama da N100bn daga kasashe 10 na waje cikin wata 6

Yadda Najeriya ta shigo da kifin sama da N100bn daga kasashe 10 na waje cikin wata 6

  • Najeriya na da wadatar ruwa da ke da dimbin damammakin kamun kifi da kiwo don amfanin gida da kuma fitarwa zuwa kasashen waje
  • Duk da haka, Najeriya ta dogara ne sosai kan shigo da kifi don biyan bukatun abinci a cikin watanni shida na farkon shekarar 2021
  • An kiyasta bukatar kifin da Najeriya ke da shi a yanzu ya kai sama da tan miliyan 3.4, inda kashi 40 cikin 100 kacal ke cika a cikin gida

Duk da yawan ruwa da ake dashi, Najeriya a cikin watanni shida na farkon shekarar 2021 ta kashe Naira biliyan 123.8 wajen shigo da kifi daga waje, Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana.

Bayanan na kunshe ne a cikin rahoton kididdigar Kasuwancin Kayayyakin Waje na NBS da ta buga a shafin yanar gizon ta.

Kara karanta wannan

Yadda Buhari yake kashe makudan biliyoyi wajen sayen motoci, yana laftowa Najeriya bashi

Yadda Najeriya ta shigo da kifin sama da N100bn daga kasashe 10 na waje cikin wata 6
Kalan kifin da ake shigo dashi Najeriya | Hoto: businessday.ng
Asali: Getty Images

Rahoton ya ce an shigo da kifi da ya kai Naira biliyan 48.28 a zangon farko sannan kuma an shigo da na Naira biliyan 75.44 a zango na biyu.

Kifayen da aka shigo da su sun hada da nau'in blue whitings, mackerel, Jack mackerel da Herrings.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya nuna cewa an shigo da kifin ne daga kasashen Rasha, Netherlands, Poland, Faroe Islands, Chile, Ireland, Lithuania, Mauritania, da Japan.

An shigo da blue whiting na Naira biliyan 62.4, da Herrings na Naira biliyan 35.53, sannan kuma an shigo da kifi Mackerel na Naira biliyan 25.75 daga watan Janairu zuwa Yuni 2021.

An shigo da mafi yawa a zangon farko lokacin da aka shigo da blue whitings da ya kai Naira biliyan 27.23 daga kasar Rasha.

Kamfanoni suna rige-rige don neman lasisin shigo da kifi

Kara karanta wannan

Kudaden shiga: Makuden da jihohi 36 da FCT suka samar na kudin shiga a 2021

Dr. Ime Umoh darakta a sashin kiwon kifi na ma’aikatar noma da raya karkara ya kuma bayyana cewa ma’aikatar ta karbi takardun neman lasisin shigo da kifi guda 200 daga kamfanoni.

Ya ce, duk da haka, yawancin takardun an hana su lasisin, inda 39 kawai suka sami lasisin shigo da kifin.

Umoh ya ce:

“Masu nema 151 ba su cika sharuddan ba, domin 39 ne kawai aka baiwa lasisin shigo da kifi a bana. Muna da bayanan wadannan masu nema, muna duba gogewarsu a matsayin 'yan kasuwa kafin mu ba da izini kuma ana aiwatar da tsarin amincewar sau daya a shekara. Zagaye na gaba na amincewa zai kasance shekara mai zuwa."

Kungiyar mata 'yan jarida sun koka kan tsadar rayuwa, sun mika bukatarsu ga gwamnati

A wani labarin, kungiyar mata ‘yan jarida ta Najeriya ta bayyana damuwarta kan yadda ake ta fama da matsalar rashin tsaro a kasar da kuma tsadar kayan abinci da iskar gas da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Motocci Fiye Da 50, Gidaje a Dubai Da Amurka: Jerin Kadarori Da Kuɗi Da Maina Ya Mallaka a Cewar EFCC

Ta bayyana korafin ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakatariyar kungiyar, Helen Udofa a karshen taron NAWOJ NEC da aka gudanar a garin Lafia jihar Nasarawa tsakanin 3 zuwa 5 ga watan Nuwamba 2021.

Kwamitin sanarwar ya bayyana Dorathy Nnaji (PhD) a matsayin Shugaba, tare da Rose Elishama a matsayin Sakatare da Nene Dung a matsayin mamba, Independent ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.