Bidiyon yadda wani mutum ya hargitsa zaman lafiyar banki kan batun BVN
- Wani dan Najeriya da ya fusata ya tada tarzoma a wani banki yayin da ya bukaci a rufe asusun ajiyarsa na cibiyar hada-hadar kudi
- Kwastoman ya nuna bacin ransa ga wata ma'aikaciyar banki inda ya bayyana burinsa na yanke hulda da bankin.
- Mutane a shafukan sada zumunta sun yi martani kan wannan tarzoma da mutumin ya tayar a harabar banki
Watakila ya gaji da hidimar su, wani dan Najeriya ya kutsa kai bankinsa domin ya bayyana ra’ayinsa na yanke hulda da su.
Mutumin da ya fusata ya hargitsa lamurra yayin da ya yi ihu da babbar murya cewa a rufe asusunsa.
A cikin wani dan gajeren bidiyon da @instablog9ja ya yada a Instagram, ana iya jin mutumin yana gunaguni game da batun BVN kuma ya fusata da kururuwa tare da cewa 'aikin banza'.
Kamar dai ba komai ba, sai ya matso kusa da ma'aikaciyar bankin ya bayyana mata bukatar a ta rufe asusun.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Duk wani kokarin da ma’aikatan bankin suka yi na kwantar masa da hankali bai yi nasara ba.
Martanin 'yan Najeriya kafar sada zumunta
manpikin01 ya ce:
"Yawancin lokuta idan ka ji "ku ba ni kudi na kuma ku rufe asusuna yanzu" Kudin da ke ciki ba komai bane face 'yan canji."
elvis___ ya ce:
"Bankuna sun iya ba da haushi, zare kudade ba tare da wani dalili ba, idan kun je wurinsu, bayan dogon layi lokacin da layin ku yazo, za ku ji sunce yi hakuri yallabai, hanyar sadarwa ta samu matsala."
sir_eltee ya ce:
"Hakika bankuna suna ba da haushi a kwanakin nan. Suna ba da sabis mara inganci kuma suna fusata abokan ciniki ♂️"
nonii_dee ya rubuta:
"Bankin Access ya kamata ya yi koyi da sauran bankunan. Wannan zai zama ni ba da jimawa ba, idan ba su gyara ba."
Hotunan tsohon mataimakin gwamna a Najeriya da ya koma noman doya shi da matarsa
Wani tsohon mataimakin gwamna a Najeriya, Emeka Sibeudu, ya kammala aikin noman doya a gonarsa. Sashen watsa labarai na Anambra ne ya yada hotunan aikin noman da ya kammala.
A cikin faifan bidiyo da aka yada, ana iya ganin tsohon mataimakin gwamnan jihar yana aiki yayin da yake kokarin jera sauwowin doyan da dama.
Asali: Legit.ng