Yan Najeriya har sun gaji da kuka, kashe-kashen rayuka ya zama ruwan dare: Yakubu Dogara
- Dan jam'iyyar APC ya bayyana cewa kowa ya rungumi kaddara yanzu kan lamarin kashe-kashe a Najeriya
- Yakubu Dogara yace bamu da tunanin zamu fada irin wannan mugun hali a tarihinmu a Najeriya ba
- Kashe-kashe da garkuwa da mutane ya jefa Najeriya cikin halin ha'ula'i musamman Arewacin Najeriya
Abuja - Tsohon Kakakin majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara, ya bayyana cewa da alamun Najeriya sun hakura da halin da suka samu kansu na kashe-kashe da garkuwa da mutane.
A cewarsa, mutane sun daina korafi da kuka kamar yadda suke yi a baya.
Dogara ya bayyana hakan ne yayin jawabi a taron da aka shirya a Cibiyar zaman lafiya na tunawa da Sultan Maccido dake Jami'ar Abuja, a cewar Thisday.
Ya ce yan Najeriya sun hakura yanzu kawai sun dau kaddara.
A cewarsa:
"Yau Najeriya na fuskantar rikicin da bata taba zato ba, saboda a tarihi bamu taba tunanin zai faru ba."
"Yanzu tamkar mun hakura da kashe-kashen da ake yi saboda yanzu ma an daina wallafa labaran kashe yan uwanmu a kafafen yada labarai."
"A matsayinmu da dalibai, malamai, da yyan siyasa, duk muna da laifi, yayinda yan kalilan dake fitowa suna magana sun yi fushi kuma sun gaji."
Amotekun ta kama mai garkuwa da mutane Labram Ibrahim yayin da yake haukan karya a Ondo
A wani labarin kuwa, jami’an tsaron Amotekun reshen jihar Ondo, sun kama wani da ake zaton mai garkuwa da mutane ne mai suna Labram Ibrahim.
Ibrahim mai shekaru 30 yana karyan hauka ne lokacin da aka kama shi, PM News ta rahoto.
An kama shi a garejin Akure da ke garin Ondo, hedkwatar karamar hukumar Ondo ta yanma da ke jihar, bayan zargin yanayin shigarsa da tafiyarsa.
A bisa ga rahotanni, Jami’an Amotekun da ke yankin, wadanda ke ta lura da shi, sun far masa lokacin da wasu mutane ke shirin daukarsa a cikin wata bakar motar jeep.
Asali: Legit.ng