Nasara daga Allah: Sojojin sun yi ruwan bama-bamai kan dandazon mayakan ISWAP tare da sabon shugabansu

Nasara daga Allah: Sojojin sun yi ruwan bama-bamai kan dandazon mayakan ISWAP tare da sabon shugabansu

  • Rahotanni daga jihar Borno sun nuna cewa sojoji sun hallaka mayakan ISWAP da yawan gaske a wani harin sama da kasa
  • A cewar wata majiya, jirgin yaƙin NAF ya yi ruwan bama-bamai ta sama kan taron yan ta'addan da ke tsammanin sabon wali na ciki
  • A halin yanzun babu adadin yawan yan ta'addan da suka mutu, amma dai rahoto yace da dama sun mutu, wasu sun jikkata

Borno - Yan ta'adda da dama sun sheka barzahu yayin da jirgin yaƙin sojin sama (NAF) ya saki ruwan bama-bamai kan taron mayakan ISWAP.

Daily Nigerian ta rahoto cewa jirgin yakin ya hallaka wasu tare da jikkata wasu da dama a Sabon Tumbun da Jibularam, ƙaramar hukumar Marte, jihar Borno.

Yan ta'addan sun gamu da ajalinsu ne ranar Jumu'a, daga harin bama-baman jirgin sojoji, yayin da suke tsaka da gudanar da taro tare da sabon shugabansu, Sani Shuwaram.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan ISWAP sun kai hari sansanin soji a Borno, suna ta musayar wuta da sojoji

Naf jet
Nasara daga Allah: Sojojin sun yi ruwan bama-bamai kan dandazon mayakan ISWAP tare da sabon shugabansu Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

Wata majiya daga cikin jami'an tsaron sirri, sun shaida wa PRNigeria cewa sojojin sun farmaki wurin taron sabon walin ISWAP, Sani Shuwaram, da manyan kwamndojinsa.

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin sun kai hari wurin taron ta sama da ƙasa, bisa haɗin guiwar NAF da kuma sojojin ƙasa.

Jami'in yace:

"An kai samamen ne bayan samun bayanan sirri, bibiya da kuma nazari da rundunar sojin sama suka yi."
"Yan ta'adda da yawan gaske sun sheka lahira, ciki har da kwamandoji, mayaƙa da kuma yan Hisbah na tsagin ISWAP."

Suwa aka tabbatar da sun halarci taron?

A wani bincike da sojojin suka yi ta ƙarƙashin kasa, sun tabbatar da cewa daga cikin manyan kwamandojin yan ta'addan dake wurin taron har da:

"Muhammed Bako, kwamndan mayaƙa na musamman (Rijal Ann), Muhammad Malumma, alkalin kungiya; Goni Mustapha, limamin ƙungiya; Muhammed Ba'ana, kwamandan kirta da sauransu."

Kara karanta wannan

Kada ku saurari abinda PDP ke fadi, so suke kawai su bata min suna: Ali Modu Sherrif ga Gwamnonin APC

A wani labarin kuma Sojojin Najeriya sun hallaka yan ta'adda 31, sun damke 71, wasu 1,186 sun mika wuya

Hedkwatar tsaro (HQ) ta bayyana irin ɗumbin nasarorin da sojojin Operation hadin kai suka samu cikin mako biyu.

Wannan dai ya biyo bayan hare-haren da rundunar sojin ta kai kan yan ta'addan ta sama da ƙasa a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262