Da dumi-dumi: Gwamnatin Buhari ta kara kudin mitar wutan lantarki

Da dumi-dumi: Gwamnatin Buhari ta kara kudin mitar wutan lantarki

  • Gwamnatin tarayya ta kara kudin mitar wutar lantarki wanda zai fara aiki daga ranar 15 ga watan Nuwamba
  • A yanzu farashin mita mai layi daya ya tashi daga N44,896.17 zuwa N58,661.69, inda mita mai layi uku ya tashi daga N82,855.19 zuwa N109,684.36
  • Hukumar kula da tsarin wutar lantarki ta Najeriya ce ta fitar da sanarwar a ranar Alhamis, 11 ga watan Nuwamba

Gwamnatin tarayya ta sanar da kara kudin mitar wutar lantarki masu layi daya da uku wanda zai fara aiki daga ranar 15 ga watan Nuwamba.

Ta sanar da hakan ne a cikin wata takarda mai kwanan wata 11 ga watan Nuwamba 2021, jaridar Punch ta rahoto.

Hukumar kula da tsarin wutar lantarki ta Najeriya ce ta fitar da sanarwar zuwa ga dukkan manyan manajoji, kamfanonin wutar lantarki da kuma dukkanin masu kula da mitoci.

Kara karanta wannan

An shigar da Hafsat Barauniya kotu kan amsar kudi amma taki yin aikin

Da dumi-dumi: Gwamnatin Buhari ta kara kudin mitar wutan lantarki
Da dumi-dumi: Gwamnatin Buhari ta kara kudin mitar wutan lantarki Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Sanarwar mai lamba NERC/MAP/GEN/751/2, na dauke da taken ‘Bita kan farashin mitocin wutar lantarki karkashin tsarin kula da mita ta kasa’.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ruwayar PM News, hukumar ta kara farashin mita mai fuska daya daga N44,896.17 zuwa N58,661.69.

Ta kuma kara farashin mita mai layi uku daga N82,855.19 zuwa N109,684.36.

Gyaran hanyoyin wutar lantarkin fadar Aso Rock za ta lamushe N2.5bn a kasafin kudin 2022

A wani labari na daban, mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya na bukatar majalisar tarayya ta amince da kashe N5.2b don gyaran wutar lantarki na fadar shugaban kasa a 2022.

An samu wannan lissafin ne cikin kasafin shekara mai zuwa wacce aka gabatar gaban majalisar tarayya a watan Oktoba, Leadership ta wallafa.

Mutane da dama su na ta surutai a kan yawan kudaden. Duk da dai a shekarar 2021 an ware N3.854b don gyaran wutar lantarkin.

Kara karanta wannan

2022: INEC ta yi kasafin N1.3bn don kyautar jana'iza, kirsimati da sauransu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng