An kama matan auren da ta bar gidanta zuwa wata unguwar don satar akuya
- Jami'an NSCDC a jihar Osun sun kama wata mata, Suliyat, mai 'ya'ya uku da ake zargi da satar akuyoyi a unguwar Ayepe
- Matar ta yi nasarar sace akuyar tana hanyar ficewa daga unguwar ne sai wasu suka tare ta a hanya suka mata tambayoyi kuma ta amsa cewa sata ta yi
- Matasan unguwa na daf ta fara yi mata duka ne sai jami'an hukumar NSCDC suka isa wurin da abin ke faruwa suka karbe ta don zuwa a yi bincike
Jihar Osun - Rundunar tsaro ta NSCDC reshen jihar Osun, a ranar Alhamis ta ce ta kama wata matar aure mai suna Suliyat, kan satar akuya.
Rahoton The Punch ya ce mai magana da yawun rundunar, Daniel Adigun, ya ce wacce ake zargin ta bar gidanta da ke Ilobu zuwa Ayepe a Osogbo, inda ta aikata laifin.
Kafin a kama ta, Adigun ya ce akwai rahotannin cewa dabobi suna bata a unguwar da aka kama wacce ake zargin kamar yadda ya zo a rahoton na The Punch.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya yi bayyanin cewa wacce ake zargin ta yi nasarar sace akuyan kuma tana kan hanyarta na ficewa daga unguwar ne aka kama ta.
Adigun ya kara da cewa mazauna unguwar suna daf da su fara dumama mata jiki ne sai jami'ansu suka isa wurin.
Wani sashi na sanarwar ta ce:
"A ranar 9 ga watan Nuwamban 2021, an kama wata mata mai suna Suliyat, mai shekaru 30, mai 'ya'ya uku, wacce ta yi ikirarin tana sana'ar tireda kuma mazauniyar Ilobu, karamar hukumar Irepodun a jihar Osun a Ayepe, Osogbo, inda ta tafi satar akuya.
"A yayin da ta ke hanyar fita da akuyar daga unguwar, an tare ta a hanya aka mata tambayoyi inda ta amsa cewa ta save akuayn ne."
Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba
A wani rahoton, wata kotun majistare ta daure wani matashi, Lekan Alaka, mai shekaru 19, watanni 3 bisa satar kujerun roba masu kimar N91,200 daga cocin Mount Zion Angelican.
‘Yan sandan sun kama Alaka da laifin sata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Alkali Olajumoke Somefun ya yanke hukunci bisa tabbatar da laifin da ya aikata bisa ruwayar Vanguard.
Asali: Legit.ng