Kutsen gidan Odili: Malami da wanda ake zargi sun yi uwar watsi
- Binciken da aka tsananta kan kutsen da aka yi gidan Odili ya dauka sabon salo inda Malami da wanda ake zargin suka fara musayar yawu
- A cewar Lawrence Ajodo wanda da farko ya ce shi dan sanda ne, ya ce Malami ne ya aike su kuma shi mai bai wa AGF din shawara ne
- Sai dai da gaggawa Malami ya karyata hakan tare da cewa dan sandan bogi ba zai taba zama mashawarcinsa ba kuma neman bata masa suna ake yi
Abuja - Binciken kutsen da aka yi gidan alkalin kotun koli, Mary Odili ya dauka wata fuska a ranar Alhamis yayin da wanda ake zargin da antoni janar Abubakar Malami suka yi cacar baki.
Wanda ake zargin mai suna Ajodo Lawrence, wanda ya dinga cewa Abubakar Malami ne ya tura shi da mukarrabansa, ya ce shi mai bada shawara ne ga AGF Malami, Daily Trust ta wallafa.
Da Dumi: Malamin addinin musulunci da CSP na bogi na cikin mutum 14 da aka kama kan kutse gidan Mai Shari'a Odili
Ajodo wanda yayi ikirarin shi dan sanda ne mai mukamin CSP, ya sanar da hakan ne yayin da aka damke shi a Abuja.
Amma Malami ya gaggauta yi masa martani inda ya ce wanda bai san aikinsa ba, ba zai taba zama mai bashi shawara ba.
Daily Trust ta ruwaito cewa, hukumar 'yan sandan Najeriya a jiya ta kama wasu wadanda ta ce "Yan sandan bogi ne goma sha hudu da suka kutsa gidan Mai shari'a Mary Odili" a ranar 29 ga Oktoba.
'Yan sandan bogin sun samu jagorancin wani Ajodo ne wanda bayan an kama shi ya ce shi ba jami'in dan sanda bane.
Sauran wadanda ake zargin kamar yadda 'yan sanda suka sanar su ne: Michael Diete-Spiff, Bar. Alex Onyekuru, Bayero Lawal, Barista Igwe Ernest, Aliyu Umar Ibrahim, Maimuna Maishanu, Ayodele Akindipe, Yusuf Adamu, Bashir Musa, ASP Mohammed Yahaya, Stanley Nkwazema (dan jarida), Shehu Jibo, Abdullahi Adamu da L/CPL Mike.
An kwashe su zuwa bangaren binciken manyan laifuka na hukumar 'yan sandan da ke Garki a Abuja, kamar yadda Frank Mba, mai magana da yawun rundunar ya sanar.
Ba ni da alaka da shi, Malami
Jim kadan bayan 'yan sanda sun cafke shi, AGF ya musanta ikirarin Ajodo.
A wata takarda da Dr Umar Gwandu ya fitar, mai magana da yawun Malami ya kwatanta bayanin da "Kagaggen yunkurin tada hankula tare da janyo cecce-kuce maras tushe".
Ina tare da minista Malami: Mutumin da ya jagoranci samamen gidan Odili ya magantu
A wani labari na daban, Lawrence Ajojo, daya daga cikin masu laifin da aka kama kan farmakin da aka kai gidan Justis Mary Odili, ya ce shi mai bayar da shawara ne ga Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Ajojo, wanda ya yi ikirarin cewa shi babban dan sanda ne ya fadi hakan a lokacin da aka gurfanar da shi a Abuja a ranar Alhamis, 11 ga watan Nuwamba.
Yan bindiga sun farmaki gidan mai shari’ar na Abuja a ranar 29 ga watan Oktoba. Lamarin ya haifar da cece-kuce. Wasu mutane sun alakanta shi da Malami wanda ya nesanta kansa daga harin.
Asali: Legit.ng