Gumi ya caccaki 'yan aware: Igboho da Kanu ne suka kunna wutar rikicin Fulani a kudu
- Babban Maalamin addinin Islama, Sheikh Gumi, ya bayyana yadda 'yan aware suka lalata alakar juna
- Ya ce, Sunday Igboho da Nnamdi Kanu ne suka haddasa wutar rikici a kudancin Najeriya baki daya
- Ya ce, abubuwan da ke faruwa basu kai ga har a fara da'awar raba kasar ba, kawai dai a cewarsa rashin fahimta ne
Babban Malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi, ya zargi shugabannin ‘yan aware biyu; Nnamdi Kanu da Sunday Igboho – da laifin tada rikici a kudancin Najeriya.
Kanu, shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) da Igboho da ke kira ga kafa kasar Yarbawa dukkansu suna tsare a hannun gwamnati, Sahara Reporters ta ruwaito.
Yayin da hukumar DSS ke tsare da Kanu a Najeriya bayan an dawo da shi daga Kenya, Igboho yana gidan yari a Jamhuriyar Benin, bayan kama shi da aka yi a kasar da ke yammacin Afirka a lokacin da yake yunkurin sulalewa kasar Jamus.
Sheikh Gumi a lokuta da dama ya na kare ‘yan bindigar da ke kashe mutane, yana mai cewa bai kamata a ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya gana da ‘yan bindiga da dama a maboyarsu a yankin Arewa maso Yamma.
A cewar Gumi, sace-sacen mutane da kashe-kashen da ake dangantawa da wasu Fulani makiyaya a Kudancin Najeriya bai isa ya sa 'yan aawaren su nemi ballewa daga kasar ba.
Gumi ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa ta yanar gizo mai taken; “Musulunci da rawar da malaman addini suka taka wajen samar da zaman lafiya a rikicin ‘yan bindiga a Arewa maso yammacin Najeriya”.
Malamin ya ce:
“Kuma wani abin da na lura a Kudu shi ne, akwai bambanci tsakanin matakin ilimi da sanin ya kamata. Kuma idan akwai irin wannan rashin daidaito, rikici ba zai taba karewa ba saboda da wuya mutane su fahimci juna.
“Don haka rigingimun Fulani a Kudancin Najeriya, ’yan awaren Kanu da Igboho ne suka yi amfani da shi a matsayin daya daga cikin dalilan da suka haddasa tada zaune tsaye.
"Babu shakka, rikicin wani fage ne na wannan rikicin. Tada kura ne kawai: Fulani nawa ne suka sace mutanen da za su haddasa ballewa? Bafullatani nawa aka yiwa kisan gilla aka kashe a wadannan jahohin da za su haddasa da ballewa?”
'Yan jaridan da suke kiran 'yan bindiga 'yan ta’adda ne asalin 'yan ta’addan
Sheikh Gumi ya bayyana cewa ‘yan jaridar da suke kiran ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ne asalin ‘yan ta’addan.
Kamar yadda Arise News ta ruwaito, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da gidan Talabijin din Arise ta yi da shi, ya ce akwai bukatar a rungumi ‘yan bindiga a al’umma.
Daya daga cikin mai gabatar da shirin ya bayyana yadda ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda suke yayin da ya tambayi malamin abinda suke so kafin su zubar da makaman su.
Mayaudarin dan Oduduwa: Sheikh Ahmad Gumi ya caccaki Fani Kayode bayan komawa APC
A wani labarin, shahrarren Malamin addini, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa tuni ya san Femi Fani Kayode mayaudari kuma makaryacin banza ne.
Gumi yayi martani ne kan sauya shekar Femi Fani Kayode jam'iyyar All Progressives Congress APC daga Peoples Democratic Party PDP a shafinsa na Facebook.
A cewar Gumi, Fani-Kayode dan damfara ne kuma wuta zai shiga idan bai tuba ba.
Asali: Legit.ng