Ku gaggauta dawo da hanyoyin sadarwa a jihar Katsina, Yam majalisau ga Gwamnati

Ku gaggauta dawo da hanyoyin sadarwa a jihar Katsina, Yam majalisau ga Gwamnati

  • Majalisar dokokin jihar Katsina ta yi kira ga gwamnatin jiha ta sassauta matakin datse sadarwa a wasu sassan jihar
  • Majalisar ta yi wannan kira ne bayan wani mummunan hari da yan bindiga suka kai Batsari, inda suka kashe mutum 11
  • A cewar yan majalisun matakan musamman na datse sadarwa yana kara munana yanayin rashin tsaron jihar

Katsina - Mambobin majalisar dokokin jihar Katsina sun yi kira ga gwamnati ta sake nazari kan matakan da ta ɗauka a ɓangaren tsaron jihar.

Dailytrust tace yan majalisun sun yi wannan kira ne domin sake duba matakan musamman na datse hanyoyin sadarwa a wasu sassan jihar.

Wannan ya biyo bayan kudirin da ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Batsari, Jabir Yusuf Yauyau, ya gabatar na gaggawa yayin zaman ranar Laraba.

Karfen sabis
Ku gaggauta dawo da hanyoyin sadarwa a jihar Katsina, Yam majalisau ga Gwamnati Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Honorabul Yauyau ya gabatar da kudirin ne bayan wani mummunan hari da yan bindiga suka sake kai wa yankinsa, inda suka kashe mutum 11 wasu 13 suka jikkata.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai harin daukar fansa, sun kashe wasu matan aure tare da kone gidaje a Taraba

Meyasa suke son a maida sadarwa?

Yayin da yake gabatar da kudirin a gaban takwarorinsa, Honorabul Yauyau yace:

"Babban abin damuwar shine babu sabis din sadarwa da mutanen Batsari zasu samu damar sanar da hukumomin tsaro yayin da maharan ke cin karen su babu babbaka."
"Saboda haka ina kira ga gwamnati ta sake duba matakan tsaron da ta ɗauka, musamman lamarin sabis ɗin nan. Rashin sadarwa na ƙara munana lamarin."

Shin ya samu goyon baya?

Bugu da ƙari ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Matazu, Alhaji Ibrahim Umar, yace a wannan rana yan bindiga suka sace mutum 5 a mazaɓarsa.

Ya shawarci gwamnati da ta samar da wata hanyar sadarwa, ta yadda mutane zasu sanar da jami'an tsaro idan irin haka ta sake faruwa.

Mafi yawan yan majalisun da suka samu damar tofa albarkacin bakin su, sun shawarci ɓangaren zartarwa ya sake nazari kan wasu matakan tsaro da aka ɗauka.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bi gida-gida a Katsina, sun hallaka mutane tare da kone dukiyoyi

Wane mataki majalisa ta ɗauka?

Bayan sauraron mahawara, majalisa ta umarci kwamitin tsaro ya tuntuɓi hukumomin tsaro kan lamarin.

Hakanan kuma an umarci kwamitin ya haɗa rahoto ya kawo wa zauren majalisa ranar Talata mai zuwa, domin daukar mataki na gaba.

A wani labarin kuma Sojojin Najeriya sun hallaka yan ta'adda 31, sun damke 71, wasu 1,186 sun mika wuya

Hedkwatar tsaro (HQ) ta bayyana irin ɗumbin nasarorin da sojojin Operation hadin kai suka samu cikin mako biyu.

Wannan dai ya biyo bayan hare-haren da rundunar sojin ta kai kan yan ta'addan ta sama da ƙasa a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262