Kano: Mata ta garzaya kotun shari'a ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda murguɗa baki
- Mata ta gurfanar da mijin ta gaban Alkali Munzali Tanko na kotun musulunci mai zama a Kofar Kudu da ke jihar Kano don a raba auren su sakamakon hayaniyar da ke tsakanin su
- An samu rahotanni akan yadda matar ta ce mijinta ya na yi wa iyayen ta rashin mutunci yadda ya ga dama, ciki har da murguda mu su baki
- A bangaren mijin kuwa cewa ya yi kawai matar ta na neman hanyar rabuwa da shi ne don dama ya na zargin ta da yin auren kashe wuta ta koma gidan tsohon mijin ta
Jihar Kano - Mata ta maka mijin ta gaban kotu don bukatar a raba auren su sakamakon yadda rikici da tashin hankali ke aukuwa tsakanin su.
Ta bayyana gaban Alkali Munzali Tanko na kotun musulunci da ke zama a Kofar Kudu a birnin Kano don gabatar da korafin ta bisa ruwayar Dala FM.
Kamar yadda ta ce, mijin na ta ya na ci wa iyayen ta mutunci kuma ba ya ganin darajar su ko kadan kamar yadda ya zo a ruwayar na Dala FM.
Ta kara da bayyana yadda ya ke murguda mu su baki saboda tsantsar rashin kunya da rashin nuna da’a gare su.
Mijin ya musanta zargin
Sai dai a bangaren mijin ya musanta duk zargin da matar ta sa ta ke yi masa inda ya ce kazafi ne kawai ta lailayo ta maka mishi.
Ya bayyana wa kotun cewa tana son rabuwa da mijin ta ne don kawai ta koma gidan tsohon mijin ta.
Har ila yau, ya kwatanta auren sa da ta yi a matsayin auren kashe wuta, don cimma manufar ta.
Zugar Ƙawaye Na Bi: Ku Taya Ni Roƙon Mijina Ya Mayar Da Ni, Tsohuwar Matar Babban Sarki a Najeriya
A wani labarin, jun ji cewa Olori Damilola, tsohuwar matar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi ta fito fili ta bai wa basaraken da gidan sarautar hakuri.
A wata takarda wacce ta wallafa ta shafin ta na Instagram a ranar Lahadi, sarauniyar ta bai wa gabadaya ‘yan uwan Adeyemi hakuri da kuma majalisar jihar Oyo.
Damilola, wacce ita ce amaryar basaraken, ta zargi gidan sarautar da nuna halin ko-in-kula akan ta da dan ta daya tal.
Asali: Legit.ng