2022: INEC ta yi kasafin N1.3bn don kyautar ta'aziyya, kirsimati da sauransu
- Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta ware N1.3 biliyan saboda kyautar ta'aziyya, bikin kirsimeti da sauransu
- Ta mika wannan bayanin ne daga cikin kasafin kudin hukumar da aka tura gaban kwamitin kula da hukumar a majalisa
- Mahmud Yakubu ya koka da yadda ake kokarin ware N100bn na zaben 2023 wanda yace ko a 2019 an ware N189bn don haka ba zai isa ba
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta ware N1.3 biliyan domin walwalar ma'aikatan ta a shekarar 2022.
Wannan ya hada da kyautar ta'aziyyar ma'aikatanta, kyautar kirsimeti da sauran alawus da ma'aikata da sauransu za su amfana, Daily Trust ta wallafa.
Hukumar ta bayyana kasafin ta gaba daya N140 biliyan inda ta mika shi gaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da INEC wanda ke samun shugabancin Sanata Kabiru Gaya.
Kamar yadda ya nuna: "Tsarikan walwala da jin dadin ma'aikatan hukumar za su hada da kyautar jana'iza ko ta ta'aziyya, alawus din kaiwa da kawowa, alawus din Kirsimeti da sauransu."
Bayanin ya nuna cewa, za a yi amfani da N107 miliyan da wasu gyare-gyare, N160 miliyan na man fetur, hadurran zabe da sauran alawus za su kwashe N11.6 biliyan, Daily Trust ta wallafa.
N11.6 biliyan na hadurran zabe da sauransu ya na da banbanci da N600 na inshora ta rayuwa ga ma'aikatan hukumar zaben.
A makon da ya gabata ne, Farfesa Mahmood Yakubu yace ana son ware N100 biliyan domin yin zaben 2023 a cikin kasafin kudin shekara mai zuwa wanda hakan yayi kadan sosai.
A yayin jawabi bayan bayyana gaban kwamitin INEC na majlisar dattawa domin kare kasafin 2022, Yakubu ya ce N189bn aka ware domin zaben 2019, don haka na 2023 ba zai zama N100bn.
Ya ce, "A yanzu muna magana da ma'aikatar kudi kan bukatar kari a kasafin zaben 2023. Za mu bukaci kudi sosai kuma mun kara rumfunan zabe kuma za mu kawo sabbin tsarin fasaha. Yawan masu kada kuri'a zai karu sama da 84 miliyan."
Gyaran hanyoyin wutar lantarkin fadar Aso Rock za ta lamushe N2.5bn a kasafin kudin 2022
A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya na bukatar majalisar tarayya ta amince da kashe N5.2b don gyaran wutar lantarki na fadar shugaban kasa a 2022.
An samu wannan lissafin ne cikin kasafin shekara mai zuwa wacce aka gabatar gaban majalisar tarayya a watan Oktoba, Leadership ta wallafa.
Mutane da dama su na ta surutai a kan yawan kudaden. Duk da dai a shekarar 2021 an ware N3.854b don gyaran wutar lantarkin.
Asali: Legit.ng