Bidiyon yadda dattijuwa ta shiga hannu yayin da aka cafke ta da jaririn sata
- Wata dattijuwa ta shiga hannun fusatattun matasa bayan samunta dauke da jaririn sata
- Da kyar aka kwace ta daga hannun matasan bayan sun gano cewa jinjirin da take dauke da shi na sata ne
- Sai dai kuma dattijuwar matar ta bayyana cewa sun hadu da mahaifiyar yaron ne inda ta bata wasu yan kudade kadan ita kuma sai ta mallaka mata yaron
Jihar Anambra - Fusatattun matasa sun far ma wata dattijuwar mata bayan an kama ta dauke da jariri sabon haihuwa da ta sato.
Labarin wanda shafin lindaikejiblogofficial ya rahoto ya nuna cewa da kyar aka kwaci matar mai suna Roseline daga hannun matasan bayan kama ta da suka yi da jinjirin a yankin Upper Iweka, Onitsha, jihar Anambra.
A cewar idon shaida, jinjirin bai fi dan sati guda ba kuma ba a san wacece mahaifiyarsa ba.
Da Duminsa: Dalibai sunyi barazanar tsayar da harkoki cak a Zaria saboda sace ma'aikatan kananan hukumomi 13
Da aka yi mata wasu tambayoyi, dattijuwar wacce ta fito daga jihar Enugu amma mazauniyar Onitsha, ta yi ikirarin cewa ta hadu da uwar dan a Asaba, jihar Delta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Roseline ta kara da cewa bayan haduwarsu sai ta ba uwar jinjirin wasu yan kudade kadan inda ita kuma ta bar mata dan.
Ga bidiyon kamar yadda shafin lindaikejiblogofficial ya sanya a Instagram:
Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a a kan wannan al'amari.
bmgonstage ta ce:
"Wasu mutane dai sun dauki wannan mummunan aiki a matsayin kasuwanci. Bawan Allah."
longrich_mia ta yi martani:
"Najeriya kasa ta, Allah ya shiryi Naija."
kokolete ta ce:
"Me za ta yi da jinjirin? ko kuma za ta wallafa ne a Facebook cewa Allah ya bata da tana da shekar 64?"
nenpinrit ta ce:
"Abun bakin ciki wannan kasuwanci ne na yau da kullun a kasar nan safarar jarirai..Allah na tare da jinjirin me zai sa uwa ta siyar da dantaba zan iya shafe minti 30 ba tare da ina kusa da jinjirina ba."
An tsinci sassan jinjiri da aka yi gunduwa-gunduwa da shi a Kano
A wani labari na daban, mun ji cewa an tsinci sassan jikin wani jinjiri da aka datsa gunduwa-gunduwa a unguwar Sakau a garin Wudil na jihar Kano a ruwayar Daily Trust.
Mazauna Sakau a Sabon Gari da ke Wudil sun ce sun farka a safiyar Lahadi sun tsinci sassan jikin jinjiri, yana mai cewa an tsinci kafufuwa da kai a wurare daban-daban cikin sunkoro.
Mai unguwar Sakau, Mallam Muhammadu Sule, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce sun sanar da hukumomin tsaro da yan sanda domin a gudanar da bincike.
Asali: Legit.ng