Da dumi-dumi: Jami’an tsaro sun hana lauyan Kanu, yan jarida da shugabannin Ibo shiga harabar kotu
- Yayin da aka dawo zama don ci gaba da shari'ar shugaban kungiyar awaren IPOB, jami'an tsaro sun hana lauyan Kanu, yan jarida da shugabannin Ibo shiga harabar kotu
- Har ila yau an hana sauran masu fafutuka shiga cikin dakin da ake shari'ar Nnamdi Kanu
- Sai dai kuma sauran lauyoyinsa da suka hada da Ifeanyi Ejiofor da Aloy Ejimakor sun samu shiga cikin kotun
Abuja - A ranar Laraba, 10 ga watan Nuwamba, jami'an tsaro sun hana Maxwell Opara, daya daga cikin lauyoyin shugaban kungiyar awaren IPOB, Nnamdi Kanu, shiga harabar babban kotun tarayya da ke Abuja.
Hakazalika an hana yan jarida da shugabannin kabilar Igbo da sauran masu fafutuka shiga dakin shari'ar, jaridar Punch ta rahoto.
Sai dai kuma, rahoton ya nuna cewa an bar sauran lauyoyin da suka hada da Ifeanyi Ejiofor da Aloy Ejimakor sun shiga cikin dakin shari'ar.
Da Duminsa: Dalibai sunyi barazanar tsayar da harkoki cak a Zaria saboda sace ma'aikatan kananan hukumomi 13
A ruwayar Daily Trust, ta ce ma’aikata da yan jaridar da sunayensu ke cikin jerin wadanda za su nadi shari’ar sun samu shiga harabar kotun.
Justis Binta Nyako ce ta dage shari'ar Kanu zuwa yau Laraba.
Kanu na fuskatar tuhumar da ta shafi ta'addanci kuma ya kasance tsare a hannun rundunar tsaro ta farin kaya tun bayan da aka sake kama shi daga wata kasar ketare a watan Yunin 2021.
Bai amsa tuhume-tuhume bakwai da ake masa ba a gurfanar karshe da yayi a kotu a ranar 21 ga watan Oktoba.
Ba mu da hannu a kama Nnamdi Kanu, gwamnatin kasar Kenya ta fadawa kotu
A gefe guda, mun kawo a baya cewa gwamnatin kasar Kenya ta kara nisanta kan ta daga kama shugaban haramtaciyyar kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra ta IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, rahoton Vanguard.
Gwamnatin yayin kare kan ta a kotun da dan uwan Kanu, Kingsley Kanunta Kanu ya shigar da kara a maimakon shugaban IPOB din, gwamnatin kasar Kenya ta ce ba da izinin hukuma gwamnati ta kama Kanu ba.
Takardar da lauyan Kanu na musamman, Aloy Ejimakor ya gabatar wa Vanguard a maimakon dan’uwan Kanu ta nuna bayan zaman kotun ranar 2 ga watan Nuwamba ta nuna hakan.
Asali: Legit.ng