Ba zamu yarda da dokar hana wa'azi da El-Rufa'i ke kokarin kafawa ba, Kungiyar CAN

Ba zamu yarda da dokar hana wa'azi da El-Rufa'i ke kokarin kafawa ba, Kungiyar CAN

  • Shekaru bayan kafa dokar tantance wa'azi, gwamnan Kaduna ya kafa majalisa ta musamman a jihar
  • Kungiyar Kiristocin Najeriya ta bayyana cewa sam ba zasu yarda da wannan dokar inda suka kira ta da azzaluma
  • El-Rufa'i yace an kafa kwamitin ne don tabbatar da Malamai ba sa wa'azin haddada rigima tsakanin jama'a

Makurdi - Kungiyar Kiristocin Najeriya, reshen jihar Benue, a ranar Talata ta yi Alla-wadai da dokar tantance wa'azi da Malamai da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa.

Shugaba CAN na Benue, Rabaran Akpen Leva, ya bayyanawa manema labarai cewa Gwamnan jihar Kaduna, Nasir EL-Rufa'i, na kokarin yaki da Ubangiji, rahoton NewTelegraph.

Rabaran Akpen yace da ban haushi mutum yayi kokarin kafa dokar yaki da wa'azin Kiristoci saboda hakan fito-na-fito ne ga addinin Kirista a Najeriya da duniya gaba daya.

Kara karanta wannan

Kungiyar PDP ta nemi Gwamna Wike ya nemi takarar kujerar shugaba Buhari a 2023

Yace:

"Wannan fito-na-fito ne da Coci. Gwamnan jihar Kaduna ta samar da wannan doka a baya amma yayinda mutane suka caccakeshi sai aka ajiye kuma aka manta da shi amma yanzu kawai aka dawo da shi kuma aka tabbatar da shi."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ba zamu yarda da wannan doka ba. Wannan yaki da Ubangiji ne. Duk wani mai tunani a Najeriya zai yi mamakin ta yaya mutum zai ce zai tantance wa'azi."

Kungiyar CAN
Ba zamu yarda da dokar hana wa'azi da El-Rufa'i ke kokarin kafawa ba, Kungiyar CAN Hoto: Governor of Kaduna
Asali: UGC

El-Rufa'i ya kafa majalisar tantance wa'azi da Malamai masu wa'azi a jihar Kaduna

Gwamnan Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna ya kafa majalisar tantance Malamai masu wa'azin addini a fadin jiharsa don tabbatar da cewa wanda ya cancanta kadai za'a bari yayi wa'azi.

A taron rantsar da mambobin majalisar da akayi ranar Juma'a, 15 ga Oktoba 2021 da ya gudana a gidan Sir Kashim Ibrahim, El-Rufa'i yace addini alaka ne tsakanin mutum da ubangijinsa, ba abin amfani wajen neman matsayin siyasa ko kudi ba.

Kara karanta wannan

An kai sabon hari a Kaduna, an kashe mutane an ƙone gidaje da dama

Hakazalika yace addini ba abinda za'a rika amfani da shi wajen lalata dukiyan juna da kashe-kashe rayuka bane.

Wani aiki majalisar zata yi?

Yayin jawabi da mambobin majalisar da ya ranstar, El-Rufa'i yace suna da hakkin tabbatar da cewa Malaman addini basu haddasa rikici tsakanin jama'a.

A cewarsa, mambobin kwamitin su tantance masu wa'azi don tabbatar da ko mutum ya cancanta yayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng