Bidiyon Maina yana dariya a kotu bayan yanke masa ɗaurin shekaru 8 a gidan yari ya janyo cece-kuce

Bidiyon Maina yana dariya a kotu bayan yanke masa ɗaurin shekaru 8 a gidan yari ya janyo cece-kuce

  • Bayan yanke wa Abdulrasheed Maina hukuncin shekaru 8 a gidan gyaran tarbiyya, an gan shi ya na murmushi a wani bidiyo yayin da ya ke barin kotun
  • Wannan lamari ya shayar da mutane da dama mamaki inda daruruwan ‘yan Najeriya su ka dinga cece-kuce a kafafen sada zumunta
  • Wasu su na mamakin yadda ya ke murmushi bayan a matsayin sa na tsohon shugaban hukumar fansho an kama shi dumu-dumu da lamushe N2b na ‘yan fansho

Abuja - Babbar Kotun Tarayya, Abuja a ranar Litinin 8 ga watan Nuwamba ta yanke wa Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar Fansho na kasa, shekaru 8 a gidan yari bayan kama shi da laifin halasta kudin haram na Naira biliyan 2.

Kara karanta wannan

Lamari ya yi muni yayin da matasa suka ba hammata iska, suka datse hannayen juna

Alkalin kotun, Okon Abang, bayan gamsuwa da cewa Maina ya saci naira biliyan 2 na ‘yan fansho, “wadanda da yawan su sun rasu ba tare da sun mori gumin su ba.”

Bidiyon Maina yana dariya a kotu bayan yanke masa ɗaurin shekaru 8 a gidan yari ya janyo cece-kuce
Maina yana dariya a kotu bayan yanke masa ɗaurin shekaru 8 a gidan yari ya janyo cece-kuce. Hoto: EFCC/Premium Times
Asali: Facebook

Alkalin ya kuma umarci kwace wasu kudade da kadarorin Maina.

Saidai an ga tsohon shugaban hukumar fanshon ya na nuna halin ko in kula a kotu inda aka ga ya na dariya hadi da murmushi a wani bidiyo da Premium Times da BBC News Yoruba su ka wallafa.

An hango Maina ya na ta murmushi yayin da jami’an hukumar gidan gyaran hali su ke tafiya da shi.

Bidiyon ya janyo cece-kuce iri-iri daga ‘yan Najeriya daban-daban a kafafen sada zumunta.

Martanin wasu daga cikinsu

Wani Arigu Ariso Audu ya ce:

Kara karanta wannan

Shekarun sun yi kadan: Martanin yan Najeriya a kan hukuncin da kotu ta yanke wa Maina

“Dariya ya ke yi bayan an yanke masa hukunci. Ubangiji ya taimaki talaka.”

Aiku Adegboyega ya ce:

“Ina tabbatar da cewa mutumin nan ba zai yi shekara 1 ba a gidan yari kafin Malami ya bukaci a sassauta ma sa. Ban taba ganin jami’in gidan yari ya na tallafa wa mai laifi irin wannan. Ana girmama mutumin da ya cuci ‘yan fansho. An dai ji kunya.”

Kingsley Onyeke ya ce:

“Ya za ayi a yanke wa mai laifi shekaru 8 a gidan yari kuma ya sa kayan alfarma ya na murmushi ba tare da an daure hannun sa ba. Wannan karamin shiri ne ko da gani.”

Onyenobi Chinwendu Samuel ya ce:

“Ya kamata ace Maina ya dinga kuka maimakon dariyar da ya ke yi zai wuce gidan gyaran hali.. abin nan ya ba ni mamaki.”

Idorenyin Udoh ya ce:

“Kalli yadda ya ke dariya, ko don bai sha mari ba ba ne. Ji yake yi kamar wani fitaccen mutum wanda ya ke daga wa masoyan sa hannu. Ya tabbata ba za a taba ganin wasu biliyoyin da ya lamushe ba har abada. Na san ba zai dade a gidan yari ba.”

Kara karanta wannan

An kaure tsakanin jami'an EFCC da na gidan yari kan wa zai tafi da Maina magarkama

Kotu ta janye belin Faisal Maina, ta bukaci a damko shi

A wani labarin, babbar kotun tarayya ta Abuja, ta umarci a kama yaron tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina, Faisal, bayan kin bayyanarsa a kotu don a cigaba da shari'a a kan zargin ha'inci da ake masa.

Alkali mai shari'a, Okon Abang, ya umarci jami'an tsaro da su kama Faisal duk inda suka gan shi. Kotun ta gayyaci wani dan majalisa mai wakiltar mazabar Kaura-Namoda, Umar Galadima, don ya bayyana a gabanta ranar Laraba.

Kotun ta umarci ya bayyana don ya bayar da hojojin da za su hana a kulle shi ko kuma ya biya naira miliyan 60 na beli ga gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164