Kudaden shiga: Makuden da jihohi 36 da FCT suka samar na kudin shiga a 2021

Kudaden shiga: Makuden da jihohi 36 da FCT suka samar na kudin shiga a 2021

  • Jihohin kasar nan sun bayyana kwazo a shekarar 2021 inda suka tatso tare da samar da kudin shiga a kasar nan har N849.123 biliyan
  • Wasu daga cikin hanyoyin da aka samu kudin sun hada da harajin ma'aikata, harajin kai tsaye, harajin kan tituna da na ma'aikatu da cibiyoyin gwamnati
  • Kamar yadda NBS ta bayyana, jihar Legas ce a kan gaba inda ta samar da kudin shiga har N849.123, FCT, Ribas da Kano ke biye da ita

Jihohi talatin da shida da babban birnin tarayya sun samar da kudi har N849.123 biliyan na kudin shiga a shekarar 2021, wanda ya bayyana cigaba fiye da na 2020 inda aka samu N612.87 biliyan.

Wani rahoton da hukumar kiyasi ta NBS ta fitar, ya bayyana cewa an samu N398 biliyan a wata ukun farkon shekarar 2021 kuma an samu N450 biliyan a wasu karin wata ukun, lamarin da ke nuna cigaba da kashi 13.21, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Motocci Fiye Da 50, Gidaje a Dubai Da Amurka: Jerin Kadarori Da Kuɗi Da Maina Ya Mallaka a Cewar EFCC

Kudaden shiga: Makuden da jihohi 36 da FCT suka samar a 2021
Kudaden shiga: Makuden da jihohi 36 da FCT suka samar a 2021. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Rahoton ya karkasa kudin shiga da aka samu zuwa gida biyar: Akwai PAYE, harajin kan tituna, sauran haraji, kudaden shiga daga ma'aikatu da cibiyoyi gwamnati da kuma na kai tsaye.

Ya bayyana cewa, jihar Legas ce ta samar da kudin shiga mafi yawa har ya kai N267bn, babban birnin tarayya ke biye da N69bn sai jihar Ribas mai N57bn.

Daily Trust ta ruwaito cewa, jihar Yobe ce ta ke da mafi karancin kudin shiga N4bn; Taraba, N4.7bn; Gombe, N5.4bn.

Kudin shigan sauran jihohi a wannan shekarar su ne kamar haka: Abia, N7.5bn; Adamawa, N6bn; Akwa Ibom, N18bn; Anambra, N12.7bn; Bauchi, N9.4bn; Bayelsa, N6.4bn; Benue, N6.7bn; Borno, N9.8bn; Cross River, N14.7; Delta, N41.9bn; Ebonyi, N7.7bn; Edo, N17.6bn; Ekiti, N6.5Bbn; Enugu, N14.1bn; Imo, N9.9bn; Jigawa, N9.3bn; Kaduna, N26.4bn da Kano, N15bn.

Kara karanta wannan

Dangote da MTN ne kamfanonin da suka fi biyan haraji a Nigeria, jimmilar kudin da aka samu N289.4bn

Sauran su ne: Katsina, N7.4bn; Kebbi, N7.3bn; Kogi, N9.6bn; Kwara, N15.9bn; Nasarawa, N9.5bn; Niger, N7.9bn; Ogun, N54bn; Ondo, N17.9bn; Osun, N13.6bn; Oyo, N25.9bn; Plateau, N14.4bn; Sokoto, N8.4bn da Zamfara, N8.4bn.

Rashin tsaro: Buhari ya fito daga Aso Rock, ya ga abinda ke faruwa a gari, Bafarawa

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa ya bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya bar batun walwalar fadar sa ya kai ziyara yankin arewa maso yamma da ta’addanci ya lalata.

“Bisa tashin hankalin da muka wayi gari a kasar mu, ya kamata shugaban kasa ya fito daga fadar sa, ya sa kaki sannan ya shirya mutane ciki har da ni don su kai ziyara yankin Zamfara don ganin halin da su ke ciki”, kamar yadda Bafarawa ya shaida wa BBC Hausa a ranar Litinin.

Bafarawa ya kwatanta halin da kudu maso yamma take ciki musamman Zamfara da wasu yankin jihar Sokoto a matsayin masifa. Ya dauki nauyin nuna wa Buhari wuraren da ta’addanci ya lalata, pmnewsnigeria ta wallafa.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke wa Maina hukuncin shekaru 8 a gidan yari bayan kama shi da laifin satar N2b

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng