'Yan ta'addan ISWAP sun sace 'ya'yan gidan sarautar Askira Uba
- Miyagun 'yan ta'addan ISWAP sun yi garkuwa da 'ya'yan gidan sarautar Askira Uba har maza uku kan hanyarsu ta zuwa Maiduguri
- 'Yan ta'addan sun sace Mohammed Askira da kannansa biyu, wadanda dukkansu kannai ne ga mai martaba Sarkin Askira Uba
- 'Yan ta'addan na cigaba da cin karensu babu babbaka yayin da miyagu masu kai musu bayanan sirri ke kara kaimi
Borno - 'Yan ta'addan Islamic State of West Africa Province, ISWAP, sun sace dattijo mai shekaru 50 mai suna Mohammed Askira, tare da 'yan uwansa maza biyu daga gidan sarautar Askira Uba a jihar Borno.
PRNigeria ta tattaro cewa, an yi garkuwa da su ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Maiduguri, babban birnin jihar Borno bayan halartar wani taro a garin Askira Uba.
Majiyoyi sun sanar da cewa, dattijon mai shekaru 50 da 'yan uwansa maza biyun da aka sace duk kannai ne ga Mai Martaba Sarkin Askira Uba.
A yayin da 'yan ta'addan ISWAP suka tsananta garkuwa da mutane a yankin, jama'a sun dinga nuna damuwarsu kan yadda al'amuran masu kai bayanan sirri ga 'yan ta'adda ke hauhawa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Suna bayyana bayanin kaiwa da kawowar jami'an tsaro da sauran mutane ga kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin, PRNigeria ta wallafa.
A cikin kwanakin nan ne kungiyar ta'addancin mai tarin hatsarin gaske ta nada Wali Sani Shuwaram, mai shekaru 45 a matsayin sabon shugaban ISWAP a yankin tafkin Chadi.
Nasara daga Allah: An bindige mai garkuwa da mutane yayin karbar kudin fansa
A wani labari na daban, rundunar hadin guiwa ta jami'an tsaro a jihar Ekiti ta halaka wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne yayin da ya je karbar kudin fansa a dajin da ke tsakanin iyakar jihohin Ekiti da Kwara.
Wata majiya ta sanar da manema labarai a Ado Ekiti cewa, jami'an tsaron da suka hada da sojoji, 'yan sanda da 'yan Bangan da Sarkin Fulanin Ekiti, Alhaji Adamu Abashe, ya kafa suka yi kisan a dajin Eruku da ke jihar Kwara, Daily Trust ta wallafa.
Jami'an tsaron sun yi kwanton bauna ne a yayin da masu garkuwa da mutanen suka bukaci a biya su kudin fansa har N2.1 miliyan bayan sace wani da suka yi.
Asali: Legit.ng