Kotu ta zabi ranar zaman kan karar da Sheikh Zakzaky ya shigar kan Gwamnatin tarayya
- Shugaban akidar Shi'a Shiek Ibraheem El-Zakzaky ya shigar da gwamnatin Najeriya kotu kan take masa hakki
- Sheikh Zakzaky da matarsa sun bukaci gwamnati ta biyasu kudin takemusu hakki na kimanin bilyan hudu
- Babban kotun tarayya dake Abuja ta zabi ranar zama kan lamarin
Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta zabi ranar 19 ga Junairu, 2022 matsayin ranar sauraron karar da Shugaban akidar Shi'a Shiek Ibraheem El-Zakzaky da matarsa eenah suka shigar kan hukumar DSS da Antoni Janar na tarayya.
Alkali Inyang Ekwo, ya zabi wannan rana ne domin baiwa DSS da AGF daman martani kan zargin take hakkin dan Adam din da aka shigar kansu, rahoton Channelstv.
Sheikh Ibraheem El-Zakzaky da matarsa sun bukaci Gwamnati ta biyasu kudin asarar da aka ja musu sakamakon cigaba da rike Fasfot dinsu.
Sun bayyana cewa yayinda suka niyyar sabuntan Fasfot a ofishin hukumar shige da fice, an bayyana musu ccewa hukumar DSS ta hana.
Sun kara da cewa dukkan kokarin da suka yi don cire wannan takunkumi ya ci tura.
Sun bukaci kotu ta wajabtawa gwamnati biyansu bilyan hudu kan take musu hakkinsu na dan Adam da kuma yanci, duk da cewa kotu ta wankesu ranar 28 ga Yuli, 2021.
Har yanzu akwai ɓurɓushin harsasan bindiga a jikina da matata, Sheikh Zakzaky
Shekaru shida bayan abinda ya faru tsakanin mabiyansa da sojoji a watan Disamba 2015, Sheikh Zakzaky yace har yanzun akwai burbushin alburusan bindiga a jikkinsa, da na matarsa Zeenatu.
A wani jawabi da mataimakain kakakin ƙungiyar mabiya shi'a (IMN), Abdullahi Usman, ya fitar ranar Alhamis, yace Malam Zakzaky ya yi wannan jawabi ne yayin da ya karbi bakuncin tawagar Fastoci.
Punch ta rahoto cewa Malaman na addinin kirista sun ziyarci Zakzaky ne domin jajanta masa kan abinda ya faru, bayan babbar kotun Kaduna ta bada umarnin sakinsa.
Asali: Legit.ng