Har yanzu akwai ɓurɓushin harsasan bindiga a jikina da matata, Sheikh Zakzaky
- Shugaban mabiya aƙidar shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, yace har yanzun akwai ragowar harsashin bindiga a jikinsa da matarsa
- Shehin malamin ya yi wannan furucin ne yayin da ya karbi bakuncin tawagar malaman addinin kirista da suka ziyarce shi
- Rahotanni sun bayyana cewa Fastocin sun kaiwa malamin ziyara ne domin nuna godiyarsu kan alkairan da yake zuba wa kiristoci
Abuja - Shekaru shida bayan abinda ya faru tsakanin mabiyansa da sojoji a watan Disamba 2015, Sheikh Zakzaky yace har yanzun akwai burbushin alburusan bindiga a jikkinsa, da na matarsa Zeenatu.
A wani jawabi da mataimakain kakakin ƙungiyar mabiya shi'a (IMN), Abdullahi Usman, ya fitar ranar Alhamis, yace Malam Zakzaky ya yi wannan jawabi ne yayin da ya karbi bakuncin tawagar Fastoci.
Punch ta rahoto cewa Malaman na addinin kirista sun ziyarci Zakzaky ne domin jajanta masa kan abinda ya faru, bayan babbar kotun Kaduna ta bada umarnin sakinsa.
Meye dalilin ziyararsu ga shehin malamin?
Legit.ng Hausa ta gano cewa tawagar fastocin sun ziyarci malamin ne domin godiya a gareshi bisa ciyarwan da yake wa zawarawa mabiya addinin kirista.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wannan ziyara dai ta zo ne watanni biyu bayan kotu ta yanke hukunci, inda El-Zakzaky ya shafe shekaru 6 a tsare.
Ko meyasa El-Zakzaky yake ciyarwa?
Usman yace:
"Malam Zakzaky yace bada kyautar kayan abinci ba wani abu bane, domin zai cigaba da bayarwa ga mabuƙata."
"Ya kuma yi kira ga mutane da su kyautatawa mabukata domin fatattakar yunwa a ƙasar nan."
"Shehin malamin ya bayyana cewa har zuwa yanzun akwai ɓurɓushin harsasan bindiga a jikinsa da kuma na matarsa. Ya kuma gode wa malaman kirista bisa wannan ziyara."
Su wanene suka ziyarci Zakzaky?
Daga cikin tawagar da suka ziyarci malamin akwai, Fasto Yohanna Buru, daga Kaduna, Titus Ishaku daga Jos, John Ahmadu daga Abuja da kuma fasto Julius Audu.
A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun kashe yan sanda, Lauyoyi tare da kona fasinjojin wata mota
Rahotanni sun bayyana cewa wasu tsagerun yan bindiga sun kashe jami'an yan sanda da wasu lauyoyi a Ebonyi.
Lamarin ya faru ne a ƙauyukan Isu and Onicha Igboeze, dake ƙaramar hukumar Onicha a cikin jihar.
Asali: Legit.ng