2023: Dole kirista ne zai gaji Buhari, In ji Ƙungiyar Kirista ta PFN
- Kungiyar kiristocin Nigeria masu bin darikar Pentacostal ta ce dole ne shugaban kasa da zai gaji Buhari ya zama kirista
- Bishop Francis Wale Oke, shugaban kungiyar na PFN na kasa ne ya bayyana hakan bayan taron shugabannin kungiyar a Legas
- Oke ya ce tun dawowar demokradiyya a 1999, karba-karba ake yi tsakanin musulmi da kirista don haka a cigaba da hakan kuma yanzu lokacin kirista ne
Jihar Legas - Kungiyar Kirista ta Pentecostal Fellowship of Nigeria, PFN, ta ce dole ne duk wanda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari a 2023 ya kasance kirista domin yin adalci.
SaharaReporters ta rahoto kungiyar ta bayyana matsayarta kan batun ne ta bakin shugabanta na kasa, Bishop Francis Wale Oke, a karkshen taron shugabanninta da ake yi a Legas.
Oke ya ce a ranar Juma'a:
"Ba mu tunanin dai-dai ne a sake zaben wani shugaban kasa musulmi a 2023. Musulmi ya yi mulkin shekaru 8 kenan zuwa 2023. Coci ta bashi goyon bayan da ya kamata. Mun masa addu'a.
"Ba mu yi nadama ba. Amma, yanzu muna son shugaban kasa kirista. A yi la'akari da hakan. Kowa ya san dai-dai. Idan ka duba, tun daga 1999, abin karba-karba ake yi, Obasanjo, Yar'Adua, Jonathan sai Muhammadu Buhari. Bai kamata bayan Buhari wani musulmi ya karba ba. Hakan ba adalci bane. Mu yi abinda ya dace. Allah mai son adalci ne."
Ya kara da cewa shugabanci bai kamata ya zama lamari na kabila ko addini ba, amma ya kamata a duba abin da ke faruwa a zahiri bisa ruwayar SaharaReporters.
Ya cigaba da cewa:
"Ko ana so, ko ba a so, addini ya zama babban abin da ake la'akari da shi a siyasar Nigeria. Sune suka kawo shi, yanzu duk mun tsindima cikinsa, abinda muke cewa shine muna son shugaban kasa kirista."
Oke ya ce abin da ke magana a kai ra'ayi ne da miliyoyin 'yan Nigeria saboda haka a cigaba da tsarin da ake kai tunda 'yan siyasan sun riga sun jefa addini cikin lamarin.
Babban malamin addinin kiristan ya ce ba za su amince da wani abu ba illa shugaban kasa kirista da suke bukata.
2023: CAN ta yi gargaɗi kan tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimaki masu addini iri ɗaya
A wani rahoton kun ji cewa Shugabancin kungiyar kiristocin Najeriya ta CAN sun ja kunnen jam’iyyun siyasa akan tsayar da ‘yan takarar su duk masu addinai daya a zaben 2023 da ke karatowa.
Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito kungiyar ta ce kada duk ‘yan takarar su kasance musulmai ko kuma duk kiristoci don hakan na iya yamutsa siyasa a kasar.
Shugaban CAN, Dr Samson Ayokunle ya yi wannan jawabin ne yayin da ya jagoranci wata ziyara da su ka kai ofishin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege a ranar Alhamis.
Asali: Legit.ng