Tsohon shugaban kamfanin dillancin labaran Najeriya, Jide Adebayo, ya mutu
- Allah ya yiwa tsohon shugaban kamfanin dillancin labaran Najeriya, Jide Adebayo, rasuwa
- Marigayin ya amsa kiran mahaliccinsa a ranar Alhamis, 4 ga watan Nuwamba, bayan yar gajeriyar rashin lafiya a wani asibitin Lagas
- Aminin Adebayo, Manjo Janar Lasisi Abidoye mai ritaya, shine ya tabbatar da hakan a cikin wani jawabi a ranar Juma’a
Lagas - Tsohon mukaddashin Shugaban kamfanin dillancin labaran Najeriya, Cif Jide Adebayo, ya rasu, rahoton NAN.
Adebayo ya rasu a wani asibitin Lagas a ranar Alhamis, 4 ga watan Nuwamba, bayan yar gajeriyar rashin lafiya. Ya mutu Yana da shekaru 66 a duniya.
Wani aminin Adebayo, Manjo Janar Lasisi Abidoye mai ritaya, shine ya tabbatar da hakan a cikin wani jawabi a ranar Juma’a a Omu Aran, karamar hukumar Irepodun da ke jihar Kwara, PM News ta rahoto.
Har zuwa mutuwarsa, Adebayo ya kasance Eesa na Omu-Aran, mutum na biyu a masarautar garin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kasance babban darakta da ke kula da sashin talla, shugaban ayyukan lagas, tsohon mukaddashin shugaban NAN, kuma kwamishinan labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar Kwara a 1999.
Abioye ya bayyana Adebayo a matsayin:
“Kwararren dan jarida kuma jagora nagari wanda za a yi kewarsa sosai.
“Cif Eesa ya kasance mai son zaman lafiya kuma shugaba mara son kai. Ya kasance jagora na kwarai, mai gaskiya da kuma tsoron Allah.”
Adebayo ya fara harkar jaridarsa da jaridar Nigerian Herald a Ilorin 1974.
Hawaye sun kwaranya yayin da Najeriya ta sake rashi na wani tsohon sanata
A wani labarin, mun kawo a baya cewa, Allah ya yiwa shahararren dan siyasan Najeriya kuma tsohon sanatan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Sanata Hosea Ehinlanwo rasuwa, Sahara Reporters ta rahoto.
Tsohon dan majalisar wanda ya wakilci yankin Ondo ta Kudu a majalisar dattawa tsakanin 2003 da 2011 ya mutu a gidansa da ke Abuja bayan yar gajeriyar rashin lafiya, jaridar The Nation ta kuma rahoto.
Dan marigayin mai suna Soji ne ya tabbatar da hakan. Kuma mahaifin nasa ya rasu yana da shekaru 83.
Asali: Legit.ng