Na daina zuwa Coci saboda Faston kullum zagin Buhari yake yi, Femi Adesina

Na daina zuwa Coci saboda Faston kullum zagin Buhari yake yi, Femi Adesina

  • Mai magana da yawun Shugaban kasa ya daina zuwa bautar ubangijinsa saboda Malamin cocin na zagin Buhari
  • Femi Adesina ya bayyana cewa shekarunsa talatin yana zuwa wannan coci amma kawai ya yanke shawaran daina zuwa
  • Adesina ya kasance mai magana da yawun shugaban kasa tun lokacin da Buhari ya hau mulki a 2015

Abuja - Mai magana da yawun Shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana yadda ya daina zuwa Coci ranar Lahadi a Abuja saboda Faston na zagin Shugaba Muhammadu Buhari.

Adesina a jawabin da ya saki ranar Alhamis ya bayyana hakan.

A jawabin da ya yiwa take, 'Kumuyi fa daban yake', ya jinjinawa Fasto Williams Kumuyi na Deeper Christian Life wanda ya ce mutane su daina zagin Buhari.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya yi basaja ya kai ziyaran bazata asibiti, ya damke ma'aikata na karban kudin Haram

Adesina, duk da cewa bai bayyana sunan cocinsa ba, an gano cewa mamban Cocin Foursquare Gospel ne inda ya kasance yana zuwa tun 1988.

Na daina zuwa Coci saboda Faston kullum zagin Buhari yake yi, Femi Adesina
Na daina zuwa Coci saboda Faston kullum zagin Buhari yake yi, Femi Adesina Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

A jawabin, mai magana da yawun Shugaban kasan yace wasu Fastoci sun mayar da mimbarin wa'azi wajen zage-zage da yada kiyayya.

Yace:

"Na kasance ina zuwa wani Coci a Abuja daga 2015 zuwa 2018, kawo zuwa lokacin da Faston ya fara ganin kansa a matsayin wanda zai kawo karshen gwamnan Shugaba Buhari."
"Kowace Lahadi, zage-zage da soke-soke yake yi. Amma nayi hakuri, tun da na fi shekaru talatin ina zuwa Cocin. Sai ranar da abin ya isheni."

Adesina ya ce lokacin da aka sace daliban makarantan Dapchi, babu irin sunan da Faston bai kira shugaba Buhari da shi ba, amma da aka sako daliban bai ce komai ba.

Kara karanta wannan

Zulum ya sake bude titin Bama zuwa Banki, shekara 9 bayan rufe shi

Shugaba Buhari ya ce zai kafa wani tarihin da ba a taba ba a Najeriya kafin ya bar ofis

A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai rufe gibin kayayyakin more rayuwa a kasar kafin ya sauka a mulki.

Ya kara da cewa, sabanin gwamnatocin baya, za a yi amfani da rancen da gwamnatinsa ta karbo wajen gudanar da ayyuka domin rage yawan gibin ababen more rayuwa a kasar nan.

Shugaban ya yi magana ne ta bakin shugaban ma’aikatansa, Farfesa Ibrahim Gambari, a wajen bikin kaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta Afirka, Dokta Bamanga Tukur mai taken 'Legacies of a Legend' a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng